Musa Iliyasu Kwankwaso ya soki gwamnatin Kano kan sabbin masarautu masu daraja ta biyu

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Jigo a jam’iyyar APC a jihar kano Dr Musa Iliyasu Kwankwaso ya kalubalanci majalisar dokokin jihar bisa yadda ta amince da kudirin kirkirar masarautu masu daraja ta biyu a Kano, inda ya bayyana abun da suka yi a matsayin raina kotu.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar talata majalisar dokokin jihar kano ta amince da kudirin kirkirar sabbin masarautu masu daraja ta biyu a jihar.

Masarautun sun hadar da Gaya Rano da Karaye.

Talla

Musa Iliyasu Kwankwaso yace babbar kotun tarayya dake zamanta a kano ta umarci kowanne bangare dake cikin Shari’ar rikicin masarautun jihar da ya tsaya a matsayinsa har zuwa lokacin da zata yanke hukunci.

 

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a cikin wani shiri na sa’a guda da aka yi da shi, wanda kadaura24 ta saurara.

An Sako Mahaifiyar Mawaki Rarara Da Aka Sace

Ya jaddada cewa a fuskar shari’a cewa har yanzu Sarakuna biyar masu daraja ta daya ake da su a jihar kano. Inda ya ce ba wani batu na sarakuna masu daraja ta biyu.

” Duk da yake ni ba lauya bane, amma maganar ta na gaban kotu, kuma Sarakuna biyar muka sani, don haka a ra’ayina abun da majalisar dokokin jihar kano ta bata lokaci ne kawai, dole su jira kotu ta yanke hukunci akan batun”.

Gwamnan Kano ya nada sabbin Sarakuna 3 masu daraja ta biyu

Ya ce al’ummar masarautun Rano Gaya, Bichi da Karaye ba za su yi murna da wannan abun da majalisar dokokin jihar kano ta yi ba.

“Ta Ina al’ummar masarautun Rano Gaya da Karaye za su ji dadin wannan abun da aka kirawo doka, bayan an kaskantar da darajar masarautunsu”. Inji Kwankwaso

Musa Iliyasu Kwankwaso wanda tsohon kwamishinan ne a ma’aikatar raya karkara ta jihar ya zargi Rabi’u Musa Kwankwaso da kokarin kawo tasgaro da cikas fa cigaban jihar kano.

” Kwankwaso makiyin Kano ne, kowanne lokaci burinsa ya ga Kano ta koma baya, ya kuma ki barin gwamna na yanzu Abba Kabir Yusuf ya yiwa kano abun da ya dace ta hanyar juya gwamnan. Za ma mu iya cewa shi ne gwamnan Kano ta karkashin kasa”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Mamallakin jaridar Nigerian Tracker ya zama Ma’ajin kungiyar masu yada labarai a kafar yanar gizo ta Arewa

Kungiyar masu yada labarai a kafafen sadarwa na zamani...

Rusau: Ana zargin an harbi mutane 6 a unguwar Rimin zakara dake Kano

Daga Nazifi Dukawa   Mazauna Unguwar Rimin Zakara da ke Karamar...

Da dumi-dumi: Bayan dakatar da Sojaboy daga Kannywood, wata masarautar a sokoto ta tube rawaninsa

Masarautar Gidan Igwai ta dakatar da Usman Umar wanda...

Masu yada hotunan Akpabio a ofishin SDP suna yi ne don bata sunan Jam’iyyar – Hon. Ali Shattima

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban Jam'iyyar SDP na jihar Kano...