Gwamnan Kano ya nada sabbin yan hukumar gudanarwar Kano Pillars, ya baiwa Ahmad Musa Mukami

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nada sabbin yan hukumar gudanarwar kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar aikowa kadaura24 a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce sabbin mambobin hukumar an zabo su ne bisa kwarewa da gogewarsu kuma za su yi aiki na wucin gadi na shekara guda, tare da yuwuwar sabunta musa mukaman bisa la’akari da kwazon da kungiyar za ta yi a kakar wasanni masu zuwa.

Talla
Talla

Sabbin yan hukumar sun ƙunshi :

– Ali Muhammad Umar (Nayara Mai Samba) – Shugaba

– Salisu Kosawa – Honorary Member
– Yusuf Danladi (Andy Cole) – Memba

– Nasiru Bello – Member

– Muhammad Ibrahim (Hassan Yamma) – Member

– Muhammad Usman – Member

– Muhammad Danjuma Gwarzo – Member

– Mustapha Usman Darma – Member

– Umar Dankura – Member

– Ahmad Musbahu – Member

– Rabiu Abdullahi – Member

– Abubakar Isah Dandago Yamalash – Daraktan yada labarai

– Ismail Abba Tangalash – mataimakin daraktan yada labarai

– Engr. Usman Kofar Naisa – Member

Gwamnan ya bayyana kwarin gwiwar cewa wadannan mutane za su yi amfani da gogewar su wajen tafiyar da harkokin kungiyar ta Kano Pillars FC.

Talla

Ana sa ran sabuwar hukumar za ta yi aiki kafada da kafada da ma’aikatar matasa da wasanni ta jiha da sauran masu ruwa da tsaki a harkar wasanni domin bunkasa kungiyar Kano Pillars.

Bugu da kari, gwamnan ya amince da nada Kyaftin din Super Eagles na Najeriya, Ahmed Musa a matsayin jakadan wasanni na jihar Kano. Ya ce mukamin na sa zaburar da ‘yan wasan tare daga martabar kungiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An sanya dokar hana fita a Jigawa

An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare...

Gwamnan Kano ya bayyana abun da gwamnatin za ta yi a filin Idi

  Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar...

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...