Sabbin Sarakunan Rano da Karaye sun ziyarci Sarki Sanusi II

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Sabbin sarakunan Rano da Karaye da aka nada a matsayin masu daraja ta biyu sun yi mubaya’a ga Sarkin Kano na 16 Malam Muhammadu Sanusi II a ranar Laraba.

Sun kai wa sarki Sanusi II ziyarar ne sa’o’i kadan bayan Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana nadin nasu.

Sabbin sarakunan sun hada da: Alhaji Muhammad Maharaz na Karaye, Muhammad Isah Umar na Rano, da Alhaji Aliyu Abdulkadir na Gaya.

Talla

A wani faifan bidiyo da wakilin kadaura24 ya gani, sarakunan masu daraja ta biyu sun yi mubaya’a ga Sarki Sanusi a zaman fadar da aka gudanar a ranar Laraba.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya soki gwamnatin Kano kan sabbin masarautu masu daraja ta biyu

Duk sarakunan biyu sun yi alkawarin yin aiki a karkashin masarautar Kano mai daraja ta daya tare da gode wa Gwamna Abba Yusuf bisa ganin sun cancanta har ya nada su .

Idan za a iya tunawa, a ranar jiya talata 16 ga Yuli, 2024, Gwamnan ya rattaba hannu a kan dokar kafa masarautu masu daraja ta biyu a jihar. Masarautar Rano da ta kunshi kananan hukumomin Rano, Kibiya, da Bunkure; sai masarautar Gaya da ta kunshi kananan hukumomin Gaya, Ajingi, da Albasu; ita kuma Karaye ta kunshi kananan hukumomin Karaye da Rogo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related