Daga Sani Idris Maiwaya
Kamfanonin Amart Entertainment da kannywood Enterprises LTD da Hajiya Aisha Tijjani sun Maka hukumar tace Fina-Finai da jihar kano da shugaban hukumar Abba El-Mustapha a gaban kotu bisa dakatar da kamfanonin da hukumar ta yi a kwanakin baya.
Kamfanonin dai sun yi karar El-Mustapha ne hukumarsa a gaban babbar kotun jihar kano, Inda suka Mika wasu bukatu guda biyu a gaban kotun kuma kotun ta amince musu.
Bukatun dai sune :
1. Sun roki kotun da ta dakatar da duk wani matakin da hukumar tace Fina-Finai da shugaban ta suna dauka akan su har sai an kammala sauraron Shari’ar, kuma kotun ta amince da bukatar.
Hotunan yadda Sarkin Kano ya gudanar da Hawan Daushe
Kotun ta kuma bukaci hukumar da ta dakatar da dakatarwar da ta yi musu har sai an kammala sauraron karar da masu kara suka shigar.
2. Kotun ta umarci hukumar tace Fina-Finai da shugaban ta da kada su sake su sake shiga al’amuran da suka shafi aiyukan masu kara ta wacce fuska.
Kuma kotun ta ce masu karar suna da damar yin duk harkokin su Wanda basu Karya doka ba, don haka a basu damar yin aiyukan su.
Kotun dai ta ce zata Fara sauraren karar a ranar 29 ga watan afirilu shekara ta 2024.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito tun a wata Fabrairun wannan shekara ne hukumar tace Fina-Finai ta ce ta dakatar da lasisin kamfanonin Amart da kannywood da kuma Hajiya Aisha Tijjani sakamakon karya wasu dokokin hukumar da kamfanonin suke yi.