Da dumi-dumi: Bayan dakatar da Sojaboy daga Kannywood, wata masarautar a sokoto ta tube rawaninsa

Date:

Masarautar Gidan Igwai ta dakatar da Usman Umar wanda akafi saninsa da (SOJA BOY) daga sarautar Yariman Gidan Igwai dake jihar Sokoto da Masarautar ta bashi a baya.

A wata sanarwa da ta fito daga Marafan Sarkin adar, mai dauke da sa hannun Alhaji Abubakar Marafan, Masarautar ta ce ta tube rawanin Sojaboy saboda wasu dalilai da suka bayyana.

InShot 20250115 195118875
Talla

A cewar Sanarwar ‘An samu bidiyon sa yana aikata abubuwan da suka sabawa addini, al’ada da dabi’un mutanen Gidan Igwai. Bisa wannan dalili ne masarautar ta yanke hukuncin dakatarwa tare da tsige shi daga sarautarsa.

Waiya ya kaddamar da kungiyar masu tallata aiyukan gwamnan Kano a Facebook

Hakazalika, Sanarwar ta bayyana irin yadda al’ummar yankin su yi tir da wannan dabi’a kuma sun nesanta kansu daga wannan abu mara kyau. Da tsohon basaraken yake aikatawa a wakokinsa.

Daga karshe masarautar tayi nasiha ga tsohon basaraken akan yaji tsoron Allah ya rungumi dabi’u irin na karantarwar addinin Musulunci.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito hukumar tace fina-fina ta jihar Kano ta ce ta dakatar da Sojaboy saboda wasu bidiyoyi na badala da ya ke yadawa da sunan wakoki ko fina-finan Kannywood.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...