Daga Halima Musa Sabaru
Mahaifiyar fitaccen mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara Hajiya Hauwa’u Adamu, ta sami ‘yanci bayan shafe kwanaki 20 a hannun masu garkuwa da mutane.
Rarara ne ya tabbatar da labarin kubutar mahaifiyar tasa a sahihin shafinsa na shafin sa na Instagram a safiyar Larabar nan.

Duk da har yanzu babu cikakken bayanin yadda aka sako dattijuwar mai kimanin mai shekaru 75, amma rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce an biya wasu makudan kudade a matsayin kudin fansa kafin a Sako dattijuwar.
Gwamnan Kano ya nada sabbin Sarakuna 3 masu daraja ta biyu
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito an sace mahaifiyar mawaki Rarara ne a jihar Katsina a cikin watan da ya gabata.
A halin da ake ciki kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a baya ta sanar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da su.