Daga Zainab Kabir Kundila
kungiyar marubuta labaran wasanni ta kasa reshen jihar Kano wato (SWAN) na farin cikin sanar da nadin uban kungiyar da Sakatare da Mataimakin Sakatare biyo bayan taron da sabbin zababbun mambobin kwamitin zartaswa kungiyar suka gudanar kwanan nan.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na kano Zaharradeen Sale ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
A kokarin kungiyar kudurin SWAN na tabbatar da gudanar da kyakyawan Shugabanci, ta yi la’akari da cancanta kwarewa da Sani makamar aiki wajen zabo wadanda zasu maye wancan kurbi na manyan mukamai na Sakatare da Mataimakin Sakatare.
Wadanda aka zabar sun hadar da :
Kungiyar ta nada Muhammad Nur Tijjani a matsayin Sakatare ya kawo kwarewa da gogewa ga wannan aiki. Tare da ingantaccen tarihin aikin jarida a masana’antar wasanni, Muhammad Nur Tijjani ya shirya tsaf don inganta ingantaccen tsarin kungiyar, daidaita tsarin gudanarwa, da tabbatar da gudanar da ayyukan kungiyar cikin sauki tare da kwarewar ayyuka.
Farfesa Jega ya caccaki kotun daukaka kara kan hukuncin zaben gwamnan jihar kano
Sai Muzammil Dalhatu Yola a matsayin sabon mataimakin sakatare, wanda shi ma kwararre ne wanda yake nuna kwazo da kwarewa . A cikin wannan matsayi, Muzammil Dalhatu Yola, ya shirya sosai don tallafawa Sakataren wannan kungiya domin samun nasar kowa da kowa.
An nada Musbahu Bala Cediyar Yangurasa a matsayin uban kungiyar wato Ex-Officio, shi ma gogaggene wanda ya jima na bada gudunmawa ga wannan kungiya mai albarka a matakai daban-daban . Musbahu Bala a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaba yana da kwarewa a sha’anin Shugabanci don haka muna da yaƙinin zai taka rawa sosai wajen ciyar da kungiyar SWAN gaba.
Ƙungiyar Marubuta Wasanni ta himmatu wajen haɓakawa da samar da ƙwararrun ƴan jaridun wasanni, ta hanyar haɗa kai tsakanin membobi da jagorancin sabbin zaɓaɓɓun kwamitin zartarwarmur kungiyar .