Waiya ya kaddamar da kungiyar masu tallata aiyukan gwamnan Kano a Facebook

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya kaddamar da kungiyar masu tallata aiyukan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a Facebook.

Kadaura24 ta rawaito, yayin da yake kaddamar da su a yau lahadi, Waiya ya bayyana cewa gwamnan Kano yana aiyuka sosai don ciyar da jihar Kano gaba, amma kuma ba a yada aiyukan yadda ya kamata.

Ya bukaci ya’yan kungiyar da su yi amfani da shafukansa da kwarewar da suke da ita wajen tallata aiyukan alkhairin da gwamnan Kano yake yiwa kanawa.

InShot 20250115 195118875
Talla

” A wannan lokacin ya kamata ku sani Facebook ba wajen yin rawa da waka ba ne kadai, tun da kuna da mabiya to zaku iya amfani da shafukan naku wajen sanar da al’umma aiyukan gwamnan Kano ko kuma ilimantar da al’umma aiyukan gwamnan”. Inji Waiya

Kwamared Waiya ya baiwa ya’yan kungiyar tabbacin gwamnatin jihar Kano zata taimaka musu da kayan aiki sannan a basu horon yadda za su gudanar da aiyukan yadda ya Kamata.

Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar Abdulrahman Hamisu ya baiwa kwamishinan tabbacin za su yi aiki tukuru don yada aiyuka da manufofin gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...