Maryam ta Fim din Labarana ta bayyana kalubalen da ta fuskanta bayan fitar Shirin

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

Jarumar kannywood mai suna Fatima Husaini Abbas wacce aka fi sani da Maryam a cikin fim din Labarina ta ce ta fuskanci kalubale mai yawa bayan fuskanta ta fito a ciki shirin mai dogon zango na Labarina.

” Akwai fina-finai da nayi a baya kusan guda biyar koma sama da haka , amma ban sami kaina cikin kalubalen ba sai da fuskata ta bayyana a cikin shirin fim din Labarina”.

Fatima Husaini Abbas ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ta yi da TRT Africa Hausa a safiyar yau asabar.

Iftila’i: Goodluck Jonathan ya Mika Kokon Bararsa ga Yan Nigeria

“Akwai bidiyon wata rayinya da aka fito blongers suka ce nice bayan ni kuma na san bani bace, amma haka sukai ta yadawa har sai da mutane suka yarda cewa ni ce, hakan ya aka rika zagina da fadamin maganganu marasa dadi, babu shakka wannan abu yayi min zafi sosai”. Inji Fatima Husaini

Tace ta yafewa duk wadanda suka sanya bidiyon da sunanta da kuma wadanda zage ta da wadanda suka fada mata bakaken maganganu tun da dai a cewata duk basu sani ba.

Hukuncin Kotu: Yan Kasuwar Magani a Kano Sun koka tare da daukar mataki

Kalubale na biyo da ta fuskanta jarumar tace su dai bloggers din sun nemo wani tsohon bidiyon ta da suka yi suna rawa ita da ganinta wanda suke uwa daya uba daya, inda tace an dauki bidiyon ne tun a shekarar 2020 data gabata.

” Ina amfani da wannan damar ne nemi yafiyar duk wadanda wadancan bidiyoyin basu yi musu dadi ba, duk da cewa daya bani bace dayan kuma tsoho ne kuma da muharramina muka yi shi ” . A cewar Fatima Husaini

Jarumar tace ta yi mamaki sosai lokacin da Aminu Saira ya kirawo ta a waya yace mata yana so ya sakata a cikin shirin fim din Labarina, Wanda yana cikin mayan fina-finai masu dogon zango a wannan lokacin.

” Bayan ya fadamin na amince zan yi fim din, na shiga ruɗani lokacin da muka kama hanyar Inda za’a dauki fim din, inda tace ta dauka mafarki take , bata yarda ba sai da ta ji ance mata Action a Matsayin za’a fara daukar fim din”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...

Rundunar Sojin Amuruka ta kammala tsara yadda za ta kawo wa Nigeria hari

  Rundunar sojin Amurka da ke Afirka, AFRICOM, ta gabatar...

Kalaman Trump: Gwamnatin Nigeria ta Fara tattaunawa da Gwamnatin Amuruka

Gwamnatin Najeriya ta ce a gwamnantance tana tattaunawa da...

Ba zan bar Siyasa ba har lokacin da zan bar Duniya – Mal Shekarau

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce...