Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Shugaban Jam’iyyar SDP na jihar Kano Hon. Ali Shattima Tudun Murtala ya musanta labarin dake yawo a shafukan sada zumunta cewa shugabannin majalisar dattawan Nigeria sun Kai wata ziyara ofishin Jam’iyyar ta su.
” Yadda ku ka ga Wannan hotunan nima haka na gansu, amma abun da suke yadawa karya ce , domin tsohon hoto ne da aka dauke shi kusan sama da shekara guda data gabata”.

Hon. Ali Shattima ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa ta musamman da yayi da jaridar Kadaura24 ranar lahadi.
” An dauki hoton ne lokacin da Shugabannin majalisar Sanata Godswil Akpabio da Barau Jibrin suka ziyarci ofishin Jam’iyyar SDP kamar yadda suka ziyarci na jam’iyyun PDP da LP da NNPP domin neman goyon bayan sanatocin jam’iyyun kafin su zama Shugabannin majalisar”. Inji Hon. Ali Shattima
Babban Dalilin da ya sa na Shiga Siyasa – Sani Danja
Ya ce masu yada tsofaffin hotunan suna yin haka ne saboda sun ga yadda jam’iyyar SDP ta yunkuro domin ta karbi kasar nan.
Hon. Ali Shattima Tudun Murtala ya bukaci al’ummar Nigeria da su yi watsi da masu yada wadancan hotuna saboda suna yi ne kawai don bata Jam’iyyar SDP a wajen al’ummar Nigeria