Ƙungiyar Masu Rajin Samar da Zaman Lafiya ta Mata da Matasa ta Najeriya (Association of Nigerian Women and Youth for Peace Advocates — ANWOPA), ta karrama Shugabar Kamfanin Tura Travels and Tours Limited, Hajiya Rabi Aminu Umar, da lambar yabo ta girmamawa mai taken Certified Eminent Peace Ambassador (CPA), wato fitacciyar jakadiyar zaman lafiya.
An bayar da wannan lambar yabo ne a ranar 12 ga Nuwamba, 2026, bisa la’akari da irin gudunmawar da Hajiya Rabi Aminu Umar ke bayarwa wajen tallafawa mata da matasa, bunƙasa harkokin ilimi, samar da zaman lafiya da kuma hidimta wa al’umma ba tare da son kai ba.

Wannan karramawa na nuna irin jajircewarta wajen samar da damammaki ga mata da matasa, inganta ilimi da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma, musamman a Arewacin Najeriya.
Ƙungiyar ANWOPA ta bayyana cewa, ta bayar da wannan lambar yabo na daga cikin ƙoƙarinta na gano tare da karrama mutanen da ayyukansu na jin ƙai da gudunmawarsu ke tallafawa Wajen inganta rayuwar al’ummominsu.
Ta ce Hajiya Rabi Aminu Umar ta kasance mai ƙwazo wajen taimaka wa mata da matasa, tare da tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi da masu buƙata ta musamman ta hanyar ayyukan jin ƙai da shirye-shiryen ci gaban bil’adama.
A wajen bikin miƙa lambar yabon, Malam Faisal, mukaddashin Manajan Kamfanin Tura Travels and Tours Limited, ne ya wakilci Hajiya Rabi Aminu Umar wajen karɓar wannan gagarumar karramawa.
A jawabin da ya gabatar, Faisal ya bayyana Hajiya Rabi Aminu Umar a matsayin mace jajirtacciya kuma mai kishin al’umma, wadda ta yi fice wajen tallafa wa ci gaban al’umma, musamman mata da matasa a Arewacin Najeriya.
Ya ce Hajiya Rabi Aminu Umar tana ƙoƙarin samar da damammaki ga mata da matasa ta hanyar shirye-shiryen ƙarfafa musu gwiwa da tallafa musu domin su samu ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.
A cewarsa, halinta na taimakon jama’a da ƙudurin ɗaga darajar rayuwar al’umma sun sanya ta zama abin koyi da ƙarfafa gwiwa ga mata da matasa da dama.
Mista Faisal ya kuma nuna godiyarsa ga shugabancin ƙungiyar ANWOPA bisa ganin cancantar Hajiya Rabi Aminu Umar da wannan babbar lambar yabo, yana mai cewa karramawar ta nuna an yaba da ƙoƙarinta, jajircewarta da irin ayyukan alherin da take yi wa al’umma.
Ƙungiyar ANWOPA ta bayyana cewa tana ci gaba da gudanar da shirye-shirye da ayyuka da nufin bunƙasa zaman lafiya, haɗin kai, ƙarfafa mata, ci gaban matasa da ayyukan jin ƙai.
Ta ce bayar da lambar yabo ta Certified Eminent Peace Ambassador (CPA) ga Hajiya Rabi Aminu Umar ya sake tabbatar da ƙudurin ƙungiyar na karrama mutanen da gudunmawarsu ke taimakawa wajen gina al’umma mai zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.
Ƙungiyar ta bayyana cewa karrama Hajiya Rabi Aminu Umar ba wai bayar da lambar yabo kawai ba ne, illa amincewa da halayen tausayi, jajircewa, shugabanci na gari, karamci da hidimta wa bil’adama.
Ta ce wannan karramawa za ta zama abin ƙarfafa gwiwa ga sauran mata, matasa, ’yan kasuwa da masu hannu da shuni wajen ci gaba da ayyukan da ke inganta zaman lafiya, ilimi, ƙarfafa tattalin arziki da ci gaban al’umma mai ɗorewa.
Read also: Buhari ya Sanya Hannu a Kasafin kudin Shekara ta 2022
Read also: Inganta Ilimi: Kawu Sumaila ya Baiwa Wata Yarinya Gurbin Karatu a Jami’arsa ya Al-Istigama

A matsayinta na Shugabar Kamfanin Tura Travels and Tours Limited, wannan karramawa ta ƙara wa Hajiya Rabi Aminu Umar wani sabon matsayi a cikin tarihin ayyukanta na jin ƙai da gudunmawar da take bayarwa ga al’umma.
A ƙarshe, ƙungiyar ANWOPA ta taya Hajiya Rabi Aminu Umar murnar wannan gagarumar karramawa, tare da yi mata fatan samun ƙarin nasarori a harkokinta na kasuwanci da ayyukan jin ƙai da hidimta wa al’umma.
Muna taya Hajiya Rabi Aminu Umar murnar zama Fitacciyar Jakadiyar Zaman Lafiya (CPA).