Yadda Gwamna Abba ya yi hobbasa wajen magance matsalar Ruwan sha a Kano – Daga Kwamitin yakin neman zaben Abba da Tinubu

Date:

AN FARA SAMUN RUWAN SHA A KANO: HOBBASAR GWAMNA ABBA

Daga Kwamitin Yada Labarai da Hulda da Jama’a,

Na Kwamitin Yakin Neman Zabe

Har tsawon shekaru sama da goma a Kano, ba a taba yin wata sanarwa a hukumance cewa ruwa zai kare ba. Sai dai kawai ji akI famfunan sun dauke kuma aka daina ganin Ruwan sha a cikinsu .

Mutane na tashi da safe su bude famfo, sai su ji iska kadai. Wannan shi ne halin da Kano ta shiga. Birni mafi yawan al’umma a Afirka, da mutane sama da miliyan 20, amma suna fama da rashin ruwa.

FB IMG

Tarihin harkar ruwa a Kano bai fara jiya ba. Ya fara ne a shekarar 1927, lokacin da gwamnatin mulkin mallaka ta Turawa karkashin Sarkin Kano Abdullahi Bayero ta fara aikin gina matatar ruwa ta farko a Arewacin Najeriya – Matatar Ruwan Challawa. An kammala ta a shekarar 1930 da karfin samar da lita miliyan 20 a kowace rana, abin mamaki ne a injiniyanci a lokacin. Matatar ruwan ta na yiwa yankuna da dama hidima. Ta yi aiki babu tsayawa har tsawon shekaru 86.

Daga baya aka samu Tsohuwar Tamburawa a 1986 da Sabuwar Tamburawa mai karfin lita miliyan 150 a kullum, da manyan tafkunan ajiya guda biyar na Goron Dutse da aka gina tsakanin 1930 zuwa 1974, wadanda suka zama kamar huhun da ke raba ruwa a Kano.

Shuwagabanni masu hangen nesa ne suka gina wannan tsari. Amma sakaci na shekaru ya rusa shi.

Kafin Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf a rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023, ya riga ya fahimci tsanani da zurfin matsalar. Ya kafa kwamitin kwararru mai karfi domin tantance harkar ruwa. Rahoton da aka gabatar masa bayan ya karbi mulki ya kasance kamar rahoton fagen yaki.

Abin da aka gano abin tausayi ne kuma mai sosa zuciya. A Challawa, cikin manyan injinan samar da wuta guda shida da ke tafiyar da matatar idan dauke wutar lantarki, biyu ne kawai ke dan motsawa. Matatar Ruwa ta 1 da ta 2 sun mutu gaba daya. Ta 3 tana aiki da kashi 30% ne kawai. An sace famfunan da ke jan ruwa. An cire na’urorin kunna wuta daga dakunan sarrafawa.

An wawushe kayan lantarki na karkashin kasa. Kuma abin da ya girgiza har tsofaffin injiniyoyi, wata babbar bututun karkashin kasa mai tsawon kilomita 15.6 da ke kai ruwa zuwa Goron Dutse an tono ta an sace ta. Duk wadannan ta’annati an yi sune fa cikin shekaru da daman gaske.

A Goron Dutse, lamarin ya fi nuna alamar watsi da aka yi. Tafkunan da suka shayar da Kano har kusan karni guda sun shafe shekaru sama da 30 ba tare da digo ruwa daya ba. Sun bushe, sun fashe, sun cika da laka.

Lokacin da wannan gwamnati ta karbi mulki, Tamburawa da aka tsara ta samar da lita miliyan 150 a kullum tana aiki da kashi 27% ne saboda ambaliyar ruwa da ta lalata matatar jan ruwanta a 2022. Challawa da aka tsara ta samar da lita miliyan 220 tana aiki da kasa da kashi 30%. Dukansu da aka tsara su bayar da lita miliyan 370 a kullum, suna bayar da kasa da lita miliyan 90.

Birnin Kano kadai, a cewar Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, a ranar 25 ga Agusta, 2026, na bukatar sama da lita miliyan 750 na ruwan sha mai tsafta a kullum. Wannan adadi bisa binciken 2022 ne. Yanzu da yawan jama’a ya karu, bukatar ta fi haka. Ko da Challawa (miliyan 220), Tamburawa (miliyan 150) da Watari (miliyan 75) sun yi aiki 100%, za su iya bayar da lita miliyan 445 ne kawai a kullum, saura gibi sama da lita miliyan 300. Wannan gibi wannan gwamnati ta gada.

Sanye da takalman aikin ruwa na roba, tare da Mataimakinsa, Murtala Sule Garo, da manyan jami’an gwamnati, tare da injiniyoyi daga kamfanin CGC Nigeria Limited da CCECC Nigeria Limited, Gwamnan ya zagaya Challawa da Tamburawa. Ya ga bututun da ke malala, tsofaffin na’urorin tace ruwa da manyan famfunan da suka mutu. Kuma a nan take ya dauki matakin da zai zama tarihinsa.

Ya amince da Naira biliyan 21.29 – zuba jari mafi girma a harkar ruwa a Kano cikin shekaru 15.

Bayani dalla-dalla kuma abin tabbatarwa ne:

– Naira biliyan 9.9 ga kamfanin CGC Nigeria Limited domin cikakken gyaran Matatar Ruwan Tamburawa da matatar jan ruwan.

– Naira biliyan 11.39 ga kamfanin CCECC Nigeria Limited domin gyaran Matatar Jan Ruwa ta Challawa, matatar ruwan da kuma cikakken dawo da tafkunan Goron Dutse.

Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da aikin a ranar 28 ga Afrilu, 2026, aka kuma bayar da kwangilar a hukumance a ranar 7 ga Mayu, 2026. An ba ‘yan kwangila watanni takwas su kammala aikin.

Wannan ba gyara bane a takarda. Abin da ke faruwa ne a kasa. Saboda wannan dalili da wasu dalilai, Gwamnan ya cancanci karin wa’adi.

Kuma a ranar 29 ga Satumba, 2026, an kafa tarihi. Ya kaddamar da rabon ruwa daga Tafkin Goron Dutse bayan sama da shekaru 30 da aka watsar da shi.

Gaskiyar lamari kamar haka:

1. Tafkuna guda uku da suka hada karfin ajiyar lita miliyan 39.8 – 10m, 7.3m da 22.5m – an kwashe laka gaba daya an gyara su.

2. Babban bututun ruwa mai tsawon kilomita 15.6 daga Challawa zuwa Goron Dutse an dawo da ita da sabbin bututun karfe na zamani, an maye gurbin tsofaffin bututun asbestos na shekarun 1970.

3. An gyara na’urorin tace ruwa, na’urorin tacewa, manyan bututu da manyan famfuna, kuma an kammala gwajin aiki a tsakiyar Satumba.

4. Yanzu ana tuka ruwa daga Challawa zuwa Goron Dutse domin rarrabawa zuwa Dorayi, Kabuga, Kofar Fanfo, Jan Bulo, Rijiyar Zaki, Janguza, Dala, Kofar Mata da sauran sassan birnin.

Ranar kammala aikin da aka sanya a farko ita ce Disamba 2026, amma wannan gwamnati ta kammala kafin lokaci. Madalla da kyakkyawan aiki, Rankai dade Gwamnan Kanawa!

Bayan ayyukan cikin birni, Gwamna Yusuf yana yin abin da ya kere duk wata gwamnati da ta yi cikin shekaru goma – farfado da matatun ruwa na yankunan karkara da suka mutu.

Tara daga cikin matatun ruwa 19 na yankunan karkara da suka mutu ana gyara su. Guzugu a Kabo, da ya mutu har shekaru biyar, yanzu yana gudana zuwa Kura da Rimi Gado. Joda a Gabasawa na gudana. Matatar Ruwan Wudil da ta mutu shekaru da dama ta dawo cikin hayyacinta. An dawo da na Minjibir da Makoda.

A watan Mayu 2026, gwamnati ta fara cikakken gyaran Matatar Ruwan Watari da aka tsara ta rika samar da lita miliyan 75 a kullum amma tana aiki da kashi 50%. Da zarar ta dawo aiki 100%, Challawa da Tamburawa za su bayar da kashi 83% na ruwan Greater Kano yayin da Watari za ta bayar da kashi 17%.

Domin rage radadi cikin gaggawa, a watan Mayu 2026, Gwamna Yusuf ya amince da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana guda 166 a matsayin matakin gaggawa na farko. Kowacce na samar da lita 25,000 a kullum, jimilla lita miliyan 4.15 a kullum ga mutane 830,000 a kauyuka 21 da yankunan da ke fama da karancin ruwa.

Wannan shi ne tsarin Gwamna Yusuf – ba tare da bashin Bankin Duniya ba, ba tare da sayar da kadarorin Kano ga ‘yan kasuwa ba, ana samar da mafita daga cikin gida. Kuma ana gyara gaba, ba zargin baya ba.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Idan famfo a Kofar Mata ya fara fitar da ruwa da karfi bayan shekaru yana fitar da iska, idan yaro a Dala ya sha ruwa kai tsaye daga famfo a karon farko a rayuwarsa, idan Goron Dutse ya sake rike ruwa bayan shekaru 30, Kano ba ruwa kadai take murna ba. Kano na murnar Gwamnan da ya tabbatar da cewa mafarkin shekaru 95 da aka fara a 1927 na iya gudana har yanzu.

Wannan ba shugabanci kadai ba ne. Kyakkyawar niyyar ce ta gaskiya a aikace. Shi ya sa Kano dole ta ci gaba da gudana tare da Gwamna Abba a karo na biyu a 2027.

Comrade Mhammad Garba
Hon Ahmad Muhammad Aruwa
Malam Abba Anwar
Hon Gidado Satatima
Hon Abubakar Adamu Rano
Hon Yakubu Yarima
Hon Hafsat Habib Abubakar

Bangaren Yada Labarai da Hulda da Jama’a Na
Kwamitin Yakin Neman Zabe
Na Tinubu da Abba
Lahadi, 1 ga Nuwamba, 2026

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Tinubu Abba Gida-Gida Political Vanguard Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Tinubu Da Abba

‎ ‎ ‎Kungiyar Tinubu Abba Gida-Gida Political Vanguard ta jaddada goyon...

Yanzu-Yanzu: Gwamna Abba ya sauya wa wasu kwamishinoni ma’aikatu tare da rantsar da sabbi a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sauya...