Wasu mutane uku sun shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, inda suka nemi kotun ta bayar da umarnin wucin gadi da zai hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ɗaukar wasu matakai da suka shafi takarar gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC).
Takardar kotun ta nuna cewa waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Garba Umar Isa, Yau Nasiru da Atiku Jamilu Abubakar.
Read also: NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

A ɓangaren waɗanda ake ƙara kuwa, akwai Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da jam’iyyar NDC.
An gabatar da ƙarar ne a gaban Mai Shari’a S.A. Amobeda, a ranar Talata, 27 ga Oktoba, 2026, ƙarƙashin lambar shari’a FHC/KN/CS/440/2026.
Takardar ta nuna cewa masu ƙarar sun gabatar da buƙatar neman umarnin wucin gadi ga kotun, ta hanyar neman hana INEC, jami’anta da sauran wakilanta ɗaukar matakin da ya shafi batun da suke ƙalubalanta, har sai an kammala sauraron shari’ar.
Read also: Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP
Haka kuma, an bayyana cewa an shigar da buƙatar ne a ranar 17 ga Oktoba, 2026, kafin ta zo gaban kotun.
Sai dai kungiyar Kwankwasiyya ta yi mamakin matakin da mutanen suka dauka na shigar da ƙara a kotu domin hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) wallafa sunansa a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar.
A wani rubutu da jigo a Kwankwasiyya Yusif Kofar Mata ya fitar ya bayyana cewa mutanen da suka shigar da ƙarar ba su da wata alaƙa da su, yana mai cewa bai taɓa ganinsu ba, ko ma jin labarinsu a lokacin da ake gudanar da tsarin fitar da ɗan takarar jam’iyyar.
A cewarsa, siyasa ta shiga wani sabon salo mai ban mamaki, inda mutum zai fito kwatsam yana neman haƙƙin da, a ra’ayinsa, jama’a ba su ba shi ba.
Ya kuma nuna damuwa kan yadda aka shigar da ƙarar a Kano, tare da samun umarnin kotu a jihar, amma ba a sanar da shi ko jam’iyyarsa yadda ya kamata ba.
Kofar Mata ya jaddada cewa harkokin siyasa ya kamata a gudanar da su bisa gaskiya da bin ƙa’ida, ba tare da ɓoye-ɓoye ba.

Read also: Gwamnan Abba Gida-gida ya yi alkawarin samar da Karin birane biyu a Kano
Ya ce a halin yanzu, matakin da lauyoyinsu suka ɗauka shi ne shiga cikin shari’ar domin kare haƙƙinsu bisa tanade-tanaden doka.
Ya kuma bayyana fatan samun nasara a shari’ar.