Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta duniya, Amnesty International, ta yi kakkausar suka tare da yin Allah-wadai da harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai wa tawagar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP a ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, a kan titin Jekadafari da ke cikin birnin Gombe.
Harin dai ya zo ne a lokacin da ake zargin maharan sun yi ƙoƙarin hana ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, shiga cikin birnin Gombe.

A cewar Amnesty International, binciken da ta fara gudanarwa ya nuna cewa ana zargin maharan na aiki ne ga jam’iyyar APC.
Bidiyoyin da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun nuna yadda dandazon matasa ɗauke da makamai suka tare hanya, tare da amfani da tayoyi da suka banka wa wuta domin hana hana ababen hawa wucewa.
Haka kuma, ana zargin waɗannan ’yan daba da farfasa gilasan motocin da dama, lamarin da ya haifar da tsaikon zirga-zirgar ababen hawa a yankin.
Ƙungiyar ta bayyana cewa wannan na daga cikin munanan hare-haren siyasa da suka faru tun bayan fara shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen 2027.
Amnesty International ta buƙaci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da tabbatar da gurfanar da duk waɗanda ake zargi da hannu a harin a gaban kotu, bisa tsarin shari’a na gaskiya.
Ta kuma nuna damuwarta kan rashin samun wata hujja kawo yanzu da ke tabbatar da cewa an kama waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, domin tabbatar da zaman lafiya a harkokin siyasa.
Ƙungiyar ta gargaɗi cewa ci gaba da kai hare-hare kan jam’iyyun adawa na iya hana gudanar da harkokin siyasa cikin lumana .
Read also: Jiragen yakin Nigeria sun hallaka ‘yan bindiga da yawa a Neja
Read also: Majalisar ta amince da Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamnan Kano
Read also: Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf zai nada karin kwamishinoni guda uku

A ƙarshe, Amnesty International ta jaddada cewa tashin hankali ba shi da gurbi a tsarin dimokuraɗiyya, tare da kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da su bai wa magoya bayansu umarnin kauce wa duk wani nau’in tashin hankali a yayin gudanar da harkokin siyasa.