Ga duk mai bibiyar siyasar Jihar Gombe, tabbas zai yarda da jam’iyyar PDP ta shiga wani mawuyacin hali na siyasa da ba a taɓa ganin irinshi ba a jihar. Jam’iyyar da a baya take da ƙarfi, manyan jiga-jigai, shugabanni da dimbin magoya baya, a yau tana fuskantar mummunan koma-baya sakamakon ficewar manyan jagororinta, rushewar tsarin tafiyar da ita da kuma sauya sheƙar dumbin mambobinta zuwa jam’iyyar APC.
Abin da ke faruwa a PDP ta Jihar Gombe ba ƙaramin rikicin cikin gida ba ne, illa wata babbar alama ce ta durƙushewar tsarin jam’iyyar gaba ɗaya. Daga matakin shugabancin jiha zuwa ƙananan hukumomi, sannan har zuwa matakin unguwanni da rumfunan zaɓe, PDP na rasa mutanen da suka kasance ginshiƙai wajen tafiyar da harkokin jam’iyyar da kuma samar mata da karfin siyasa a tsawon shekaru.
Read also: Nigeria ka iya zama kamar China idan aka koma tsarin jam’iyya daya – Ganduje

Abin lura shi ne, wannan rugujewar ba ta tsaya kan wasu ƙananan mambobi ko magoya baya ba. Manyan shugabannin jam’iyyar, ‘yan takarar gwamna, tsofaffin ‘yan majalisu, shugabannin ƙananan hukumomi, jiga-jigan Yan siyasa da kuma masu gudanar da harkokin jam’iyyar suna ta barin PDP, tare da komawa APC.
Manyan Jiga-jigai Sun Juya Wa PDP Baya:
Abu mafi tayar da hankali ga PDP shi ne yadda mutanen da suka kasance fuskar jam’iyyar, waɗanda suka jagorance ta a lokuta daban-daban, har da waɗanda suka nemi kujerar gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwarta, suka fice daga cikinta.
Wasu daga cikinsu sun kasance jagororin da suka taka muhimmiyar rawa wajen gina jam’iyyar, wasu kuma sun yi takarar gwamna da ita, yayin da wasu suka riƙe manyan mukaman siyasa da na gwamnati a ƙarƙashin jam’iyyar. A yau, da yawa daga cikin waɗannan mutane sun koma APC, inda suka haɗa kai da sauran masu ruwa da tsaki wajen gina sabon tsarin siyasa na tafiyar APC. Ga sunayen wasu daga cikinsu:
1. Senator Usman Bayero Nafada
2. Alh Ahmed Yayari, Former PDP National Treasurer.
3. Alh. Audu Hamma Saleh, Former Governorship Aspirant
4. Alh. Bala Magaji
(Chairman PDP Stakeholders forum)
5. Barr. Joel Jagafa (Former PDP, State Chairman)
6. Chief. James Pisagih Former SSG
7. Buba Shanu Former PDP, State Secretary
8. Hon Sunday Danlele
9. Alh Yusuf Jigawa (PDP Chairman Nafada)
10. Alh. Idris Abubakar Yayayi (Chairman PDP Kwami)
11. Babangida Ventures
12. Hon. Kawu Abare (Deputy State Legal PDP)
13. Sheikh. Salisu Sulaiman Diouf PDP Secretary Herwagana ward
14. Abubakar M. Dalibi, Chairman PDP social Media forum
15. Muhammad Haladu PDP Zonal Chairman Gombe Central
16. Adamu Alhaji Abdu (PDP Chairman Y/Deba)
17. Alh. Idi Mai Fachi Assistant Organizing secretary)
18. Hon. Adamu Ibrahim Nono
19. Hon. Ibrahim Abubakar Sorodo (From Nafada)
20. Hon. Muhammad Babangida (Nation)
21. Umar Mohammed (Akwaye)
22. Maina Dansarki
23. Hon.Adamu Damji
24. Alh Babangida Usman, chairman of the PDP contact committee.
25. Alh Murtala Tale, Former State PRO PDP
26. Alh Nura Abba, Former deputy State Secretary PDP
27. Alh Jamilu Kalshingi, Former youth leader, PDP
28. Yamaltu Deba PDP LGA Executives.
29. Malam Hassan
Muhammad, Former Commissioner Finance.
30. Hon. Ameer Sunusin Gombe ( Founder Pantamiyya
Movement)
31. Hon. Buhari Dalhatu.
Ficewar waɗannan mutane ta haifar da babban gibi a tsarin PDP, musamman idan aka yi la’akari da cewa da yawa daga cikinsu suna da tasiri a yankunansu, suna da mabiya, kuma sun kasance masu iya tattara jama’a a lokutan zaɓe.
Haka kuma, ba shugabanni kaɗai suka bar jam’iyyar ba. Mutanen da suka kasance masu gudanar da harkokin siyasa, masu haɗa kan magoya baya, shugabannin matasa, mata da sauran ƙungiyoyin siyasa sun yi watsi da tsohuwar jam’iyyarsu. Wannan ya sa PDP ba wai kawai sunayen manyan mutane ta rasa ba, har ma da injinan da ke tafiyar da harkokinta a mafi akasarin kana nan hukumomi da mazabu a Jihar ta Gombe..
PDP Ta Rasa Ginshiƙanta, Wa Ya Rage A Cikinta?
Abin da ya fi bayyana irin halin da PDP ke ciki shi ne yadda jerin ficewar manyan shugabanninta ke ci gaba da rage mata mutane masu kima da daraja dake da tasiri a fagen siyasar jihar.
A halin da ake ciki, ana iya cewa jam’iyyar ta rasa da dama daga cikin fitattun jagororinta da suka kasance masu iya wakiltarta a matakai daban-daban. Wannan ya sa tambayar da ake yi a tsakanin masu sharhi kan siyasar Gombe ita ce: Waɗanne manyan mutane ne suka rage wa PDP waɗanda za su iya jagorantar ta, sake gina tsarinta da kuma fuskantar babban zaɓen 2027?
A halin yanzu dai, alamu sun nuna cewar babu abinda ya rage a PDP sai mutane biyu kacal. Daga Dan takarar gwamna wanda yayi kutse sakamakon giyar neman mulki, sai kuma wani jagora wanda shima yakewa jam’iyyar takara. Hasalima wannan jagora, yana cikin kunshin wadanda suke fatan cigaban Gombe da kuma samun nasarar jam’iyyar APC ba don komai ba, sai don hakan shine son cigaba da kishin jihar sa.
Read also: Dan Chinan da ya kashe Ummita ya roki kotu ta dage shari’arsa har sai ya samu lauya
Dokta Jamil Gwamna Ya Zama Matattarar Ÿan Siyasa Ma Su Kishi:
A wani ɓangaren kuma, yayin da PDP ke fama da wannan matsala, jam’iyyar APC a Jihar Gombe na ƙara samun karɓuwa da kuma haɗuwar manyan masu ruwa da tsaki a ƙarƙashin jagorancin ɗan takararta na gwamna, Dokta Jamil Isyaku Gwamna, Sardaunan Gombe.
Abin lura shi ne, wannan karɓuwa ba ta tsaya ga mambobin APC kawai ba. Mambobin PDP da ADC, da PRP da NDC da sauran masu ruwa da tsaki a siyasar jihar sun bayyana goyon bayansu ga tafiyar Dokta Jamil Gwamna.
Wannan sauyi na nuna cewa siyasar Gombe na fuskantar wani sabon yanayi, inda mutane da dama ke kallon tafiyar APC a matsayin wata dama ta haɗin kai, sabunta shugabanci da kuma gina makomar jihar.
Musamman yadda wasu daga cikin waɗanda suka yi shekaru suna adawa da APC a baya ke komawa cikinta, yana ƙara nuna irin sauyin da ya samu a tsarin siyasar jihar.
Wannan na iya zama wata babbar alama ta sauyin tunanin masu zaɓe da kuma yadda siyasar jihar ke karkata zuwa sabon tsarin haɗin kai. A yayin da wasu jam’iyyun ke fama da rikice-rikice da rasa manyan mutane, APC na ƙoƙarin faɗaɗa tsarin siyasarta ta hanyar haɗa tsofaffin abokan hamayya da sababbin masu ruwa da tsaki.
2027: Shin PDP Za Ta Iya Farfaɗowa?
Babbar tambayar da ke gaban PDP a yau ita ce ko za ta iya sake gina tsarin da ta rasa kafin babban zaɓen 2027. Domin nasarar jam’iyya a zaɓe ba ta dogara da samun ɗan takara kaɗai ba. Tana buƙatar shugabanni masu tasiri, ingantaccen tsarin gudanarwa, masu tattara magoya baya, wakilai a rumfunan zaɓe da kuma amintattun mambobi a dukkan matakan siyasa.
Idan aka yi la’akari da yawan mutanen da suka fice daga PDP, musamman waɗanda suka kasance ginshiƙan jam’iyyar a matakin jiha da ƙananan hukumomi, za mu iya cewa jam’iyyar ta makara. Domin kuwa a jihar Gombe AN YIWA PDP ZIGIDIR.
Domin a siyasa, rasa manyan shugabanni abu ne mai girma, amma rasa tsarin da ke haɗa shugabanni, mambobi da magoya baya ya fi zama babban ƙalubale.
A gefe guda, Dr Jamil Isyaku Gwamna da jam’iyyar APC na da damar cin gajiyar wannan sabon yanayi ta hanyar ƙarfafa haɗin kai, haɗa kan magoya baya da kuma tabbatar da cewa duk waɗanda suka shigo tafiyar sun samu gurbin bayar da gudummawarsu wajen gina jihar.

A ƙarshe, siyasar Gombe ta 2027 na iya zama wata muhimmiyar shaida ta yadda sauyin sheƙa, haɗin kai da rugujewar tsarin jam’iyya za su iya sauya alkiblar siyasar jiha. Ga PDP, babban ƙalubalen yanzu shi ne yadda za ta iya farfaɗowa daga wannan koma-baya. Ga APC kuwa, babban nauyin da ke gabanta shi ne yadda za ta mayar da karɓuwar da take samu zuwa ingantaccen haɗin kai da nasarar da za ta amfanar da al’ummar Gombe.
Read also: Rashin Mahaifiyar Yassar, Haj. Aisha, Babban Rashi ne ga kowa, inji Gwamna Ganduje
Ga al’ummar jihar Gombe kuwa, aikinsu shine alkalanci da duba a tsanaki, sannan su kuma fahimci manufofi da kudurorin jajirtaccen shugaba, nagari abin koyi. Al’ummar Gombe sun ce Jamil Gwamna, Sardaunan Gombe shine masa.
Ibrahim Sani Shawai
12 ga Nuwamba, 2026