Dawa Cikin Watanni Hudu! IAR Ta Samar Da Sabbin Iri Uku Domin Tallafa Wa Manoman Yankunan Da Ke Fama Da Matsalar Tsaro

Date:

‎Cibiyar bincike kan harkokin Noma dake Jami’ar Ahmad Bello (ABU) ta ce ta fitar da gajerun irin Dawa don amfani da su a wuraren da suke fama da matsalar tsaro a Nigeria.
‎
‎Dakta Muhammad Ahmad Yahaya wanda ke jagorancin binkice akan inganta sabbin irin Dawar a cibiyar binciken harkokin noma (IAR Samaru) dake Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zaria ya bayyana hakan a taron ranar Manoma (Field Day) domin nuna ire-iren nau’ukan Dawa a gonar binciken IAR Samaru.

IMG 20260704 WA0007
Talla

‎
‎Dakta Yahaya, ya ce an duba kalubalen da manoma da harkokin noma ke fuskanta kamar sauyin yanayi da matsalar tsaro musamman a arewacin Najeriya hakan ya sa Hukumar raya kasashe rainon Burtaniya wato FCDO ta bayar da tallafi domin samar da arin Dawar ga al-ummar da ke fama da karancin ingantaccen irin dawa domin samun wadataccen abinci.
‎
‎Irurrukan sun hadarda SAMSORG 52 , SAMSORG 53 da kuma SAMSORG 54 da a yanzu haka an fitar dasu ga manoma.
‎
‎Cikin manoman da suka halarci taron Uwale Balarabe wadda tace sama da shekaru goma shabiyar tana noma amman bata taba samun damar zuwa irin wannan taro ba kuma taga sabbin irurrukan da take fatan yin amfani da su bisa yadda aka inganatasu dai – dai da yanayin da ake ciki na matsalar tsaro da sauyin yanayi.
‎FB IMG
‎
‎Sarkin Bumu, Alhaji Muktar Usman, wanda yake cikin mahalarta taron ya bayyana dabon irin a matsayin cigaban da yazo dai- lokacin da ake bukata.
‎
‎”Hakika an yi tunani wajen samar da irin Dawar tunda kaga baya wuce wata hudu yake isa girbi ba kamar yadda adda ake suka Dawar ba tun farkon damuna har zuwa karshenta”.
‎
‎Idon haka babu abin da zamuce da IAR sai godiya.

LEAVE A REPLY

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-Yanzu: Hakimin Gezawa Ya Dakatar Da Mai Unguwar Hayewa

Hakimin Gezawa, Alhaji Mahmud Aliyu Yusuf, ya dakatar da...

Daga Gwanara Zuwa Gidan Gwamnatin Kwara: Wanene SYD ? Daga Mustapha Balogun

DagaDaga Mustapha Balogun A ranar 27 ga Yulin 2026, zauren...

Kotu ta yanke hukunci ga matasan da suka kashe uwa da ’ya’yanta shida a Kano

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 11 da ke...

Da dumi-dumi: Kotu ta soke takarar Atiku Abubakar

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta rushe shugabancin...