Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2027 na sama da Naira tiriliyan 1.1 a gaban Majalisar Dokokin jihar.
Gwamnan ya gabatar da kasafin ne a safiyar Laraba yayin wani zama na musamman da majalisar ta gudanar a babban zaurenta da ke birnin Kano.
Read also: Wai me Garo ya yi ne ? – Daga Abba Anwar

Da yake jawabi a gaban ‘yan majalisar, Abba Yusuf ya ce an tsara kasafin ne domin bunkasa muhimman fannoni da suka hada da ilimi, lafiya, noma da ayyukan raya birane da karkara.
Ya kuma bayyana cewa kasafin zai mayar da hankali wajen samar da hanyoyin dogaro da kai ga matasa da mata, domin inganta rayuwarsu da bunkasa tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da an aiwatar da kasafin yadda ya kamata domin inganta rayuwar al’ummar Kano da kuma cika alkawuran da ta dauka.
Read also: Buhari ya taya Tinubu murnar lashe zaben Shugaban kasa

Ya bukaci ‘yan majalisar da su gaggauta nazarin kudirin tare da amincewa da shi a kan lokaci, domin bai wa gwamnati damar fara aiwatar da ayyukan ci gaba tun daga farkon shekarar 2027.