Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Biyo bayan koken da al’ummar garin Bechi dake karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, da su ka yi ga gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusif na siyar da filin wata makarantar sakandiren mata dake yankin.
Yanzu haka Mamallakin filin da ake takardama akan sa a garin Bechi, Alhaji Sagir Isyaku Ja’en, ya bayyana asali yadda ya Mallaki filin a hannun wani Mutum Mai suna Farfesa Ibrahin Shehu, da shine ya siyar Masa da wajen, tun shekarar 2015, Kuma yana da cikakun takardun shedar mallaka daga kowace Hukumar da doka ta tanada.

Alhaji Sagir Ja’en, ya ce ya yi mamakin yadda ya ji mutane na korafi kan wannan fili, duk da cewa batun ya na gaban hukumomi don tantancewa, kuma ya kai dukanin wasu hujjoji domin tantance gaskiyar lamarin.
Wasu mutane na kokarin sayar da wata makaranta a Kano, al’ummar yankin sun nemi daukin gwamna Abba
Ya kara da cewa tun asali wannan gini da ake takardama akan sa na shedar ginin Makaranta, baya cikin gurin daya mallaka, kuma bai ce nasa bane, shi ma zai iya gina Makarantar domin al’umma su amfana” inji Alh Sagir.
Haka zalika Alh Sagir Ja”en ya yi kira ga al’ummar yankin su kwantar da hankalin su, Babu abin da zai taba ginin makarantar domin ba mallakinsa bane, kuma zai basu gudunmawar data kamata wajen gina Makarantar, Dalibai su yi karatu sosai.
“A karshe Alhaji Sagir Isyaku ya godewa al’ummar garin Bechi yadda suke kokarin kawo zaman lafiya,kwanciyar hankali, yana mai cewa insha Allahu zai tabbatar da kowa ya samu Nasara domin cigaban garin Bechi da kewaye.” Sagir Ja’en
Alhaji Sagir Ja’en ya kuma turowa kadaura24 wasu daga cikin shidar mallakar filin dake kusa da makarantar da ake takaddama akansa.