‎Rahman Legacy: Yadda Gwamna AbdulRazaq Ya Sake Gina Makomar Wasanni a Jihar Kwara

Date:

‎
‎Ci gaban wasanni bai tsaya ga lashe kofuna kawai ba. Ya shafi gina ingantattun wuraren wasanni, gano hazikan ’yan wasa, yabawa tare da saka wa wadanda suka yi fice, da kuma samar da damarmaki ga matasa.
‎
‎A Jihar Kwara, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya farfado da gasar wasannin jihar bayan shafe shekaru 15 ba a gudanar da ita ba. Haka kuma, ya kafa Hukumar Wasanni ta Jihar Kwara, tare da karfafa wasannin matasa a matakin kananan hukumomi da makarantu.

IMG 20260704 WA0007
Talla

‎
‎Gwamnatin ta kuma sauya fasalin filin wasanni na George Agbazika Innih Stadium Complex, inda aka inganta kayayyakin wasanni ciki har da Pa Gabriel Ladipo Indoor Sports Hall, da samar da ingantattun wuraren wasan squash da table tennis, tare da gyara babban wurin ninkaya mai girman Olympic.
‎
‎Sakamakon wannan kokari na gwamna Abdulrahman ya fara bayyana, domin Kungiyar kwallon kafa ta Kwara United ta sake komawa gasar NPFL, ta samu damar buga wasannin nahiyar Afirka, sannan ta kafa tarihi a shekarar 2025 bayan lashe President Federation Cup.
‎
‎Gwamnatin ta kuma biya kusan Naira miliyan 201 daga cikin basussukan da ta gada, wadanda ake bin kungiyar ta Kwara United daga ’yan wasa da masu horar da su.
‎
‎Ba a harkar kwallon kafa kadai aka mayar da hankali ba. ’Yan wasa a fannoni daban-daban, ciki har da masu wasannin nakasassu, sun samu karin tallafi, yayin da ’yan wasan da suka samu lambobin yabo a wasannin kasa ke samun kyaututtuka saboda bajintarsu.

IMG 20260704 WA0005
Talla

‎
‎Yanzu haka, gasar Kwara State Sports Festival karo na 8 ta hada ’yan wasa daga dukkan kananan hukumomin jihar 16, lamarin da ke nuna kokarin gina tsarin da zai rika gano hazakan yan wasa tun daga tushe, har zuwa matakin gasannin kasa da na nahiyar Afirka.
‎
‎Wannan ba batun wasanni kadai ba ne. Jari ne da ake zubawa cikin basira ga makomar matasan Jihar Kwara.
‎

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya sulhunta Sanata Barau da Abba Bichi

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sasanta mataimakin...

‎Rikicin Masarautar Kano: Gwamna Abba ya yi ganawar sirri da na hannun daman Sarkin Kano

‎ ‎Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gayyaci...

‎Dalilin da yasa Kwamishinan ’Yan Sandan Kano ya ziyarci Sarki Aminu Ado Bayero

‎‎Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori,...

‎INEC ta bayyana Jihohin dake kan gaba wajen yawan masu katin zaɓe

‎ ‎Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta...