Daga Rahama Umar kwaru
Wata Babbar kotun jahar Kano bisa jagorancin mai Shari’a sunusi Ado Ma’aji ta saka ranar 4 ga watan Oktoba 2022 domin sake gurfanar ɗan ƙasar Chaina nan mai suna Geng Quanrong da ake zargin sa da hallaka wata budurwa mai suna Ummukulsum Sani Buhari har cikin gidansu a birnin Kano.
A zaman kotun na wannan rana ta Alhamis wanda ake tuhuma Quarong bashi da lauya har ya roƙi kotun data ɗage shari’ar zuwa wata ranar domin ya samu lauya.
Lauya gwamnati kuma kwamishinan Shari’a na jahar Kano Barista Musa Abdullahi Lawan bai yi suka ba akan roƙon da Quarong ya yi.

Zaman na yau bai yiwuba ne sakamakon rashin lauya da wanda ake tuhuma yake da shi , kuma tuhumar da ake yi masa babban laifi ne.
Wanda lauyan Gwamnati ya roƙi kotun da ta saka ranar ci gaba da sauraran shari’ar a kusa .

A ƙarshe alƙalin kotun mai Shari’a Sunusi Ma’aji ya ɗage zaman kotun zuwa 4 ga watan Oktoba 2022 domin sake gurfanar da shi.