Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bukaci majalisar dokokin Kano da ta amince masa ya nada karin kwamishinoni guda uku a kunshin majalisar zartaswa ta jiha.
Abubawa 5 da aka cimma a zaman majalisar zartarwar Kano, bayan rantsar da Abba Gida-gida
Idab za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a kwanakin baya gwamna Abba Kabir Yusuf ya turawa majalisar Sunayen mutune 19 domin tantancewa su, kuma sun tantance tare da amincewa da su, kuma tuni ya rantsar da su .

Wannan bukata na cikin takardar da gwamnan ya aikewa majalisar dokokin Kano a zaman ta na Alhamis din nan karkashin Kakakinta Jibril Isma’il Falgore.
Mutane uku da majalisar zata tantance don nada su a matsayin kwamishinoni sun hadar da Ibrahim Jibril (Fagge) da Ibrahim Ali Namadi (Dala) da Amina Abdullahi Sani (Nasarawa).