Da ɗumi-ɗumi: NNPC ta sanar da rage farashin man fetur a Najeriya

Date:

Kamfanin NNPC Retail ya sanar da fara bayar da rangwamen N66 kan kowace lita ta man fetur ga abokan cinikinsa a gidajen mai na NNPC a fadin Najeriya.

Kamfanin ya ce rangwamen wani bangare ne na bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ‘yancin kai, kuma za a ci gaba da bayar da shi daga ranar 1 zuwa 7 ga watan Oktoban 2026.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Sai dai NNPC ta bayyana cewa domin cin gajiyar rangwamen, dole ne mai sayen man ya yi amfani da manhajar NNPC Fuel App wajen biyan kudin man a gidajen man da ke cikin shirin.

Ma’ana, idan aka sayi lita 10 na fetur, rangwamen zai kai N660, yayin da lita 20 za ta samu rangwamen N1,320.

NNPC ta kuma bukaci masu ababen hawa da sauran kwastomominta su ci gaba da amfani da manhajar a tsawon lokacin rangwamen domin cin gajiyar shirin.

FB IMG

Bayan haka, rahotanni sun nuna cewa NNPC ta kuma rage farashin man fetur a wasu garuruwa, inda farashin ya sauka daga N1,395 zuwa N1,370 kan kowace lita a Abuja da kewaye, yayin da a wasu gidajen mai a Legas aka samu farashin N1,360.

NNPC ta ce rangwamen N66 zai kare ne a ranar 7 ga Oktoba 2026.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikin Masarauta: ‎‘Yan Sanda Sun Jaddada Haramcin Hawan Daba da Hawan Dawakai ga Kowa a Kano

‎ ‎Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta sake jaddada cewa...

An kama mutane sama da 380 bisa zargin shaye-shaye a Kano – Gwamna Abba

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce hukumomi sun...

Chinese, Nigerian workers celebrate Mid-Autumn Festival

Chinese and Nigerian workers at a project site in...

‎Farfse Pantami ya sake zama dan takarar gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar PDP

‎ ‎Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya lashe sabon zaben...