An kama mutane sama da 380 bisa zargin shaye-shaye a Kano – Gwamna Abba

Date:

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce hukumomi sun kama sama da mutane 380 tare da samun hukuncin kotu kan fiye da 230 cikin watanni biyu da fara tsauraran matakan yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Hakan na ɗauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.

Ya ce gwamnatin jihar ta kafa kwamitin kar ta kwana na yaƙi da shaye-shaye da dabanci a watan Yulin 2026, tare da fitar da dokar zartarwa domin ƙarfafa yaƙi da miyagun ƙwayoyi, daba da sauran laifukan da ke da alaƙa da aikata laifi.

A cewar gwamnan, rundunar ta kuma tarwatsa wuraren sayar da miyagun ƙwayoyi da maboyar masu aikata laifuka a sassa daban-daban na jihar.

Gwamna Yusuf ya ce yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da aikata laifuka nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati, jami’an tsaro, sarakunan gargajiya, malamai, iyaye da sauran al’umma.

FB IMG

Ya kuma yi kira ga matasa da su guji miyagun ƙwayoyi, tashin hankali da aikata laifuka, su rungumi ilimi, noma, fasaha, sana’o’i da masana’antun kere-kere.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Chinese, Nigerian workers celebrate Mid-Autumn Festival

Chinese and Nigerian workers at a project site in...

‎Farfse Pantami ya sake zama dan takarar gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar PDP

‎ ‎Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya lashe sabon zaben...

‎Tinubu ya taso daga birnin Paris zuwa Najeriya bayan kammala hutu

‎ ‎Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kammala hutun aiki...

‎Sarki Sanusi ya magantu kan tsare El-Rufa’i ba tare da an ba da shi beli ba

‎ ‎Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi...