Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya lashe sabon zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP na takarar Gwamnan jihar Gombe a zaben 2027.
An gudanar da zaben ne a yau, Talata 29 ga Satumba, 2026, inda Farfesa Isa Ali Pantami ya samu nasarar zama dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Gombe.

Ga dai yadda sakamakon zaɓen ya kasance;
Adadin membobin jam’iyyar PDP da suka yi zaben fidda gwani a fadin jihar Gombe 2,555.
Sheikh Isa Ali Pantami ya samu kuri’u dubu 2,054.
Khamisu Mailantarki ya zo na biyu da kuri’u 389.
Usman Garry yazo na uku da adadin kuri’u 112.
Read also: Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas
Read also: Buhari, El-Rufai, KADCCIMA sun karrama Dangote a kasuwar baje koli
Read also: Zangon karatu na uku: Gwamnatin Kano ta sanya ranar da za a koma makarantun firamare da sakandire

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa a ranar alhamis din da ta gabata babbar kotun tarayya dake zamanta a Gombe ta rushe zaben fidda gwanin da PDP ta yi a farko wasu kura-kurai, inda ta bayar da umarnin a sake zaɓen.