‎Tinubu ya taso daga birnin Paris zuwa Najeriya bayan kammala hutu

Date:

‎
‎Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kammala hutun aiki da ya tafi Turai, inda ya bar birnin Paris na Faransa domin komawa Najeriya.
‎
‎Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

IMG 20260704 WA0007
Talla

‎
‎A cewar sanarwar, ana sa ran jirgin Tinubu zai sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas da yammacin Talata.
‎
‎Sanarwar ta ce Tinubu ya zaɓi fara komawarsa Najeriya ta Legas ne domin girmama marigayi MKO Abiola, wanda aka bayyana a matsayin gwarzon gwagwarmayar dimokuraɗiyyar Najeriya kuma wanda ake ganin ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yuni 1993.
‎
‎A ranar samun ’yancin kan Najeriya, Tinubu zai halarci bikin ƙaddamar da wani fim da aka shirya domin karrama Abiola a gidan wasan kwaikwayo na Wole Soyinka da ke Iganmu, Legas.
‎
‎Yayin zamansa a Legas, Shugaban Ƙasar zai kuma gudanar da wasu muhimman tarurruka da ’yan siyasa da abokan hulɗarsa, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
‎
‎Tinubu ya bar Abuja zuwa Turai a ranar 30 ga Agusta, inda ya shafe mako guda a London kafin ya wuce Paris.
‎
‎A Paris, Shugaban Ƙasar ya halarci liyafar cin abinci ta sirri tare da Shugaban Faransa Emmanuel Macron, sannan ya gana da wasu ’yan kasuwa, ciki har da Vincent Bolloré na Bolloré Group.

FB IMG
‎
‎A ranar Litinin kuma, Tinubu ya gana da shugaban First Holdings, Femi Otedola.
‎
‎Ana sa ran Shugaba Tinubu zai koma Abuja bayan kammala harkokin siyasarsa a Legas.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Farfse Pantami ya sake zama dan takarar gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar PDP

‎ ‎Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya lashe sabon zaben...

‎Sarki Sanusi ya magantu kan tsare El-Rufa’i ba tare da an ba da shi beli ba

‎ ‎Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi...

Kwankwasiyya ta kai ƙorafi kan zargin amfani da kotuna wajen muzgunawa yayanta a Kano

Ƙungiyar Kwankwasiyya ta shigar da ƙorafe-ƙorafe ga Babban Alkalin...

Fadar shugaban kasa ta bayyana ainahin halin da Tinubu ya ke ciki

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu...