Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta sake jaddada cewa har yanzu dokar da ta haramta hawan Daba da kuma hawan dawaki ko wasu dabbobi a fadin jihar na nan daram.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a hedkwatar rundunar da ke Bompai, Kano, ranar Juma’a.

Kwamishinan ya ce Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana haramcin duk wani nau’i na hawan Daba da hawan dawaki a fadin jihar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro, da nufin tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’umma.
Ya ce duk da wannan dokar, an samu rahotannin wasu sun karya dokar.
CP Bakori ya jaddada cewa haramcin ya shafi kowa da kowa, ba tare da la’akari da matsayi ko mukamin mutum ba.
Ya ce babban aikin hukumomin tsaro shi ne tabbatar da zaman lafiya, tsaro da bin doka a cikin al’umma, yana mai cewa ba za a lamunci duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya ko jefa rayukan jama’a cikin hadari ba.
Sharadin gudanar da Hawan Daba ko Dawakai
Kwamishinan ya bayyana cewa duk wani mutum, ma’aikata ko kungiya da ke da bukatar gudanar da wani biki da ya shafi Hawan Daba, Hawan Doki ko wasu dabbobi a jihar, dole ne ya nemi izini a rubuce daga Ofishin Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano a kalla sa’o’i 72, wato kwanaki uku, kafin ranar taron.
A cewarsa, hakan zai bai wa jami’an tsaro damar tantance yanayin tsaron taron tare da daukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Read also: Idan na zama gwamna na yi tanadin kudirori 7 da zan ciyar da Kano gaba – Salihu Tanko Yakasai
Read also: Yan Nigeria ne Matsalar Kasar nan – Buhari
Read also: Hajjin bana:Kasar Saudiyya ta karawa Nigeria Wa’adin Kai Maniyatan ta zuwa kasar

Kwamishinan ya kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su mutunta dokokin tsaro tare da ba jami’an tsaro cikakken hadin kai.
CP Ibrahim Adamu Bakori ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa hukumomin tsaro za su ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da doka, oda da zaman lafiya a fadin Jihar Kano.