Yanzu-Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bada Umarnin takaita zirga-zirga Daga jihohin Nigeria Saboda Corona.

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf, 

 Gwamnatin Tarayya ta sake dawo da Dokar takaita zirga-zirga Daga a duk fadin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT) saboda Annubar Corona.


 Wannan sabon umarnin na kulle zai fara aiki ne a tsakar daren Talata, Kamar yadda vwani mamba a kwamitin Shugabancin Shugaban Kasa (PSC) kan COVID-19, Dokta Mukhtar Mohammed, ya bayyana.


 Mohammed, wanda shi ne Shugaban Kwamitin kere-kere na Kwamitin Shugaban Kasa akan Corona, ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani a ranar Litinin din Nan a Abuja.


 Baya ga da takaita zirga-zirga da aka yi, an Kuma an Kuma Hana Duk Wani taron  jama’a da ya wuce mutane 50 a kowane lokaci.


 Hakanan za’a hana damar zuwa cibiyoyin gwamnati duk wanda baya sanya abin rufe fuska yayin da aka takaita tarurrukan gwamnati da tafiye-tafiye .


 A cewar Mohammed, gwamnati ta ba da umarnin rufe wuraren shakatawa na dare sannnan dokar hana fita a duk fadin kasar za ta fara aiki har zuwa wani lokaci.


 A nasa bangaren, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Mista Boss Mustapha, ya ce fasinjojin da suka dawo daga kasashen waje wadanda suka tsere daga wuraren kebe wadanda suka dawo Daga Wata Kasa tilas za su fuskanci hukunci fishin Hukuma.

 Mustapha, wanda kuma shi ne Shugaban PSC, ya yi Allah wadai da keta dokokin kasa da kuma karbar baki, yana mai cewa kwamitin na jiran rahoton binciken da ke gudana kuma zai sanya takunkumin da ya dace kan wadanda suka karya dokar.

1 COMMENT

  1. Wawaye ga talakawa suna fama da insecurity da azabar talauci har da wai zaku takaita zirgazirga wlh Baku da hankali Allah

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...