Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaban karamar hukumar Wudil Abba Muhammad Tukur ya ba da Umarnin sassauta duk tutocin dake fadin karamar hukumar don nuna alhini bisa rasuwar tsohon shugaban karamar hukumar Wudil, Hon. Abubakar Abdullahi Likita.
” Mun ɗauki wannan matakin don Karrama aiyukan alkhairin da tsohon shugaban karamar hukumar ya yi na aiyukan raya kasa da Gina al’umma a fadin karamar hukumar Wudil”.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran shugaban karamar hukumar Wudil Nura Mu’azu Wudil ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.
“Mun bayar da umarnin sassauta tutocin da ke cikin Sakatariyar karamar hukumar da duk wasu Hukumomi da cibiyoyin dake Wudil har na tsawon kwanaki uku (3) daga ranar Talata 17 ga watan Yuni 2025”.
Ya ce sun yi hakan ne a matsayin girmamawa da juyayi ga shugaban da ya sadaukar da rayuwarsa wajen inganta ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, da hidima ga al’ummar Wudil.
Shugaban ya bukaci daukacin ma’aikata, mazauna yankin, da shugabannin al’umma da su hada kai wajen gudanar da addu’o’in nemawa marigayin rahamar Allah subhanahu wata’ala.
Hon. Abba Muhammad Tukur ya yi masa addu’ar Allah (SWT) ya gafarta masa ya sa ya na Aljannatul Firdausi.