Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta rika sanar da Limaman masallatan juma’a dake fadin jihar duk wasu bayanai da da abubuwan da su ka shafi gwammati da kuma ci gaban jihar dan sanar da al’umma .
” Wannan gwamnatin dake karkashin gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ta na ganin kima da darajar malamai da Limaman, shi ya sa ta ba a taba jin ta ci zarafi ko wulakanta wani malami ba, don haka ya ba da tabbacin gwamnati za ta cigaba da kyautata alarta da malaman.
Kwamishinan ma’aikatar yada labarai Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a yayin taron karawa juna sani na kwanaki biyu da ma’aikatar yada labarai da hadin gwiwa da ma’aikatar addinai su ka shiryawa limaman masallatan juma’a na Kano.
Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ya bukaci malaman da su san irin kalaman da za su rinka amfani da su a kan membarin masallatan su domin isar da sako ga al’umma, saboda da tasirin da jawabin malaman ke da shi ga al’umma.
Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji
” Saboda kimar ku a cikin al’umma mu ka ga ya dace mu hada kai da ku wajen isar da sakon gwamnati ga al’umma saboda yakinin da mu ke da shi, na cewa al’umma gamsuwa da bayanan da kuke yi musu”. Inji Waiya
Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce malaman su bude kirazansu domin amfani da abubuwan da za a tattauna, sannan ya roke su da su baiwa gwamnati shawarwari za su amfanar da ita don cigaban al’ummar jihar Kano.
A jawabinsa mai martaba Sarkin Kano na 16 Malam Muhammad Sanusi II ya bukaci malaman da a hudubobinsu su rika mai da hankali wajen fadawa al’umma muhimmancin zaman lafiya da hadin kan Musulmi.

” Bai kamata malamai su rika mai da hankali kan sukar juna ko nuna banbancin akida ba, kamata ya yi ku mai da hankali wajen koyawa al’umma yadda za su yi addini da kuma fadawa gwamnati gaskiya don kyautata rayuwar al’umma”.
Da yake jawabi shugaban majalisar Limamam masallatan Juma’a na Kano Sheik Muhammad Nasir Adam ya ce, daga cikin tsarin da su ke da shi basa baiwa shugaba kamar gwamna ko sarki shawara a kan mambari sai dai suje su same shi a gida dan baiwa mutum shawara a bainar Jama’a kamar kunyata shi ne ko tozartar shi.
Malaman addinin musulunci da Limaman masallatan juma’a da dama ne dai suka halarci taron bitar na kwanaki biyu da ma’aikatar yada labaran ta shirya hadin gwiwa da ma’aikatar addinai ta Kano, inda akai jawabai masu yawa kan yadda za a samar da hadin kai tsakanin su tare da nuna yadda za a rinka isar da sakonni ga al’umma.