Daga Muhammed B. Garba
Fadan daba yayi sanadiyar mutuwar wani matashi a unguwar Gayawa dake yankin karamar hukumar Unggogo, a jihar Kano.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar da misalin karfe biyu 2:00 na rana lokacin da ake tsaka da gudanar da wasan gangi wanda daga bisani ya rikide ya koma fadan daba har ta kai ga sanadiyar rasuwar daya daga cikin matasan.

Matashin mai suna Abbani dan kimanin shekaru 27 da haihuwa ya rasa ransa ne a lokacin da aka fara wasan gangi a dai-dai karfe 2:00 na rana a unguwar Gayawa.
Shugaban Karamar hukumar Wudil ya ɗauki nauyin ɗalibai 33 da za su karanci aikin Ungozoma
A cewar wata majiya da ta nemi Kadaura24 ta sakaye sunanta, ta ce Abbani shi ne wanda ya fara bude taro da addu’a irin tasu ta kauraye. Daga bude taro da addu’a ne wani matashi Mai kimani shekaru 27 da haihuwa wanda har kawo wannan lokaci ba’a fayyace sunansa da unguwarsa ba, ya yi kan marigayin da wata zabgegiyar takwabi, kai kace dama da akwai wata kulleleya a tsakaninsu, kafin kace meye har ya kai Abbani kasa Kamar rago nan take ya sa wuka a wuyan marigayin kamar yadda ake yanka akuya ya ja kuma ya yanka, sai ga jini kawai ya fara malalowa kasa.

A nan ne wasu daga cikin matasan sun garzaya da dashi asibiti amma kafin su je rai ya yi halinsa Kamar yadda aka shaidawa majiwarmu
Wannan lamarin ya farune a dai-dai lokacin da al’ummar jihar Kano ke fuskanta fadan daba da sata wata, Lamarin da yasa ake ta yin kira ga gwamnatin jiha karkashin jagoracin Abba Kabir Yusuf da ya yi kokarin kawo karshen fadan Daba a fadin jihar Kano da kewaye.