Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), ƙarƙashin jagorancin Kwamared Alhassan Yahaya, ta bayyana Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, a matsayin ɗaya daga cikin fitattun shugabanni da za ta karrama da lambar yabo ta musamman, a wani babban taron murnar cika shekara 70 da kafuwar ƙungiyar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kano ta fitar, inda ta bayyana cewa an zaɓi Gwamna Yusuf ne domin karramawa da lambar yabo ta “Media Friendly Award”, saboda irin gudummawar da yake bayarwa wajen haɓɓaka harkokin ci gaban ƙasa, ƙarfafa shugabanci nagari, da kuma jajircewarsa wajen kare martabar ‘yan jarida da ‘yancin fadar albarkacin baki.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “NUJ ta yi la’akari da irin jagorancin gaskiya da adalci da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke gudanarwa, musamman goyon bayansa ga kafafen yaɗa labarai da yadda yake nuna kishin kare dimokuraɗiyya. Wannan ne ya sanya kungiyar ta bayyana shi a matsayin gwarzon shugaba da ya dace da wannan lambar yabo.”
Ciyaman din Wudil ya ba da umarnin sassauta Totoci saboda rasuwar tsohon shugaban K/H
An shirya mika lambar girmamawar a ranar Asabar, 21 ga Yuni, 2025, a babban dakin taro na NUJ da ke birnin tarayya Abuja, a wani biki na musamman da za a gudanar domin tunawa da shekaru 70 da kafa kungiyar.
A nasa bangaren, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana jin daɗin Gwamnatin Jihar bisa wannan babban karramawa, tare da bayyana cewa wannan ya sake tabbatar da irin kulawar Gwamna Yusuf ga walwalar ‘yan jarida da muhimmancin ‘yancin fadar albarkacin baki a karkashin tsarin dimokuraɗiyya.
Kwamishinan ya kuma jaddada kudurin gwamnatin jihar na ci gaba da kare ‘yancin kafafen yaɗa labarai, tare da ba su cikakken goyon baya don su ci gaba da taka rawa wajen gina ƙasa da wayar da kan al’umma.