Daga Munnira Ahmad
Al’ummar unguwar Dorayi dake karamar hukumar Gwale a jihar Kano sun koka da yadda fadan daba ke kara tu’azzara a yankin wanda har ya tisalta musu hade Sallar magariba da isha’i a jiya lahadi .
Wani mazaunin yankin da Jaridar Kadaura24 ta zanta da shi bisa Sharadin boge sunansa, ya ce a jiya lahadi fadan daba ya tilastawa wasu masallatan yankin Dorayi Karama, zuwa konannen gidan mai da Karshen waya hade Sallar magariba da ta Isha’i.

” Lamarin fadan daba ya Zama abun da ya Zama domin wasu masallatan akan idona suka rika hade Sallar Magariba da Isha saboda yadda yaran suke cin karensu babu babbaka a yankin mu, kuma har yanzu an ki a dauki wani mataki da zai magance matsalar”. Inji shi
Ya ce fargaba da firgice ne suka tilastawa mutane daukar Wannan matakin na hade wadannan salloli.
Fadan daba: An yi wa wani matashi yankan Rago a Gayawa
Sai dai majiyar ta mu ta shaida mana cewa limamin masallacin almuntada dake unguwar ta Dorayi Sheikh Aminu Library ya ce shi ba zai hade Sallar Magariba da isha’i ba saboda fadan daba.
Inda ya ce wajibi ne mutane su Kare kawunansu tunda hukumomin da Lamarin ya shafa sun gaza magance matsalar da ya jima tana ci wa al’ummar yankin tuwo a kwarya .
Ya bukaci mahukunta da su tashi tsaye domin sauke nauyin da Allah ya dora musu na Kare rayuka da dukiyoyin al’ummar da suka zabe su.