Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnatin jihar Kano ta nuna takaicinta akan yawaitar fadace fadacen daba a birnin Kano da kewaye dake sanadiyar rasa rayukan jama’a.
Sai dai gwamnatin Kano ta alakanta fadan dabar da siyasa da ta ke zargin wasu yan hamayya da rura wutar rikicin dabar domin bata sunan gwamnatin.

Kwamishinan kananan hukumomi na Kano, Hon Muhammad Tajuddeen othman ne ya bayyana hakan a lokacin da ake tambayarsa kokarin da gwamnatin kano ke yi don magance fadan Daba ta cikin wani shiri Mai suna ”Gwamnati da jama’a” wanda aka gudanar a tashar Rahma Radio da ke Kano.
Kwamishinan ya yi zargin wasu daga cikin yan siyasa da daukar nauyin fadan Dabar a birnin Kano domin cimma wata manufa ta su ta siyasa.
Kwacen waya: Ya kamata gwamnatin Kano da hukumomin tsaro su tashi tsaye – Auwal Danlarabawa
Hon. Tajuddeen othman ya tabbatarwa da jama’ar Kano cewa gwamnati na iya kokarin ta wajen magance matsalar ta hanyar daukar matasa aikinyi da sanyasu a makarantu.
Kwamishinan ya kuma shaida cewa kwamatin da gwamnatin kano ta kafa na magance fadan Daba karkashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar kimiya da fasaha Dr Yusuf Ibrahim Kofar Mata na aiki dare da rana domin samar da tsaro a Kano.
Idan za’a iya tunawa daga ranar laraba zuwa safiyar Juma’a da Asabar fadacen fadacen dabar da kwacen waya yayi salwantar rayuwakan matasa biyu a birnin Kano ,Inda kuma fadan dabar ya hana jama’a sakat a cikin birnin.
Kwamishinan ya shaida cewa tabbatar da kare rayukan jama’a da dukiyoyin mutanan Kano na daga cikin kudurin gwamna Abba Kabir Yusuf tun kafin hawansa mulkin Kano.