Daga Rahama Umar Kwaru
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria, Sanata Barau I. Jibrin, ya kai ziyara filin wasan kungiyar kwallon kafa ta Barau a ranar Litinin, gabanin fara tunkarar gasar ajin ƙwararru ta kasa ta Kasa ta shekarar 2025.
Sanata Barau ya samu rakiyar karamin ministan gidaje da raya birane, Hon. Yusuf Abdullahi Atta, shugaban ma’aikatansa, Farfesa Muhammad Ibn Abdullah, mai ba shi shawara ta musamman kan matasa da wasanni, Kabiru Ado Lakwaya, da sauransu.

A wata sanarwa da jami’in yada labaran kungiyar Ahmad Hamisu Gwale ya aikowa Kadaura24, Sanata Barau ya yabawa kungiyar kwallon kafa ta Barau FC da ta samu tikitin shiga gasar ajin ƙwararru ta kasa, sannan kuma ya bayyana baiwa kungiyar gudunmuwar naira miliyan biyu a matsayin goron Sallah.
Sanata Barau ya bada tabbacin cigaba da baiwa kungiyar kwallon kafa ta Barau FC goyon baya har sai kungiyar ta samu nasarar shiga gasar firimiya ta Najeriya NPFL a kakar wasa mai zuwa.
“Mun zo nan ne domin mu ziyarce ku da kuma zaburar da ku matasa ‘yan wasan kungiyar ta Barau FC, burina shi ne in ga wannan kulob din yana cikin manyan kungiyoyin kwallon Kasa a Najeriya har ma a duniya, da yardar Allah zan ba ku goyon baya ta kowace hanya don samun cigaba da samin nasara,” inji shi.
Fadan Daba a Birnin Kano, Laifin Waye? – Barr. Hadiza Nasir
Hukumar gudanarwar kungiyar ta Barau FC ta karbi bakuncin mataimakin shugaban majalisar dattawa karkashin jagorancin shugaban kungiyar Ambasada Ibrahim Shitu Chanji, memban hukumar Alhaji Abdul AP, Daraktan wasanni, Yahya Muhammad, sakataren kungiyar Umar Lawan, da kuma mai kula da kungiyar, Aliyu Lawan.
Haka kuma a yayin ziyarar akwai Babban Mai horar da kungiyar, Rabi’u Tata; Mai horar da kungiyar, Madu Muhammad, Mataimakin mai horarwa, Surajo Mukhtar, Mai horar da masu tsaron gida, Babangida Muhammad.
Da yake jawabi a madadin ‘yan wasan, Usman Maidubji ya bayyana matukar godiya ga Sanata Barau Jibrin bisa goyon bayan da yake bai wa kungiyar, inda ya bayyana hakan a matsayin wani muhimmin al’amari na ci gaba da samun nasarar kungiyar.
Kungiyar Barau FC na ci gaba da shirye-shiryen tunkarar gasar ajin ƙwararru TA kasa mai zuwa, inda za ta kara da wasu kungiyoyi bakwai domin samun damar shiga gasar Premier ta Najeriya a kakar wasa mai zuwa.