Kungiyar Kwadago ta yi Watsi da Batun Karin Kudin Man Fetur

Date:

Kungiyar Kwadago ta kasa NLC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yin watsi da shirin kara farashin man fetur a Nigeria.
 Shugaban Kungiyar, Kwamared Ayuba Wabba ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja.
 A cewarsa, Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Malam Mele Kyari, ya sanar da cewa man fetur zai iya tsada har N340 daga watan Fabrairun 2022.
 Solacebase ta rahoto cewa Wabba ya bayyana Matakin da Gwamnatin tarayya ta dauka na cewa gwamnati zata Rika baiwab ‘yan Najeriya miliyan 40 Naira 5,000 a matsayin abin da zai magance illar karuwar farashin man fetur.
 Ya ce jimillar kudaden da suka ce zasu Rika baiwa Yan Kasa ya zarce kudaden da gwamnati ta ce tana kashewa a halin yanzu kan tallafin man fetur.
 Shugaban NLC ya ce duk wani yunkuri na kwatanta farashin man fetur a Najeriya da sauran kasashen duniya zai Zama kuskure ne domin Kamar ka kwatanta tuffa da mangwaro ne

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...