Daga Sani Idris Maiwaya
Rikicin Masarautar kano ya na neman daukar wani Sabon salo, saboda yadda aka zargi magoya bayan Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero da kai farmaki Fadar Sarkin Kano na 16 Malam Muhammadu Sanusi dake kofar kudu a ranar Lahadin da ta gabata bayan da Sarkin ya dawo daga gidan Marigayi Alhaji Aminu Dantata .
Wannan zargin na cikin wata sanarwa da sashin yada labarai Masarautar Kano wadda Sadam Yakasai ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.

Yakasai ya ce, “Sun fasa kofar ne suka far wa masu gadin, inda suka jikkata wasu daga cikinsu, suka farfasa motocin ‘yan sandan da ke cikin fadar, da gangan Aminu ya biyo ta titin fadar sarkin maimakon daga koki ya hanyar da zata Kai shi gidan Nasarawa amma sai a biyo ta Wannan hanyar .
“Ba Wannan ne ba karon farko da ya Fara biyo hanyar ba, ya yi hakan a baya lokacin da ya ziyarci gidan sa na Mandawari, kuma yana yin hakan ne domin ya tsoratar da mutanen yankin,” in ji Yakasai.
Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC
Kadaura24 kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Sarkin kano na 15, Abubakar Kofar-Naisa, Kan wannan batu sai har lokacin hada Wannan rahoto ba mu same a da wayarsa ba.
Sai dai wani da lamarin ya faru a kan idonsa mai suna Muktar Dahiru, inda ya karyata labarin Yakasai kuma ya ce lamarin ya faru ne tsakanin wadanda ya bayyana a matsayin ‘yan bata-gari a fadar Kofar-Kudu da kuma magoya bayan Aminu Ado Bayero.
Da dumi-dumi: Sanarwa ta Musamman daga Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai SKY
Dahiru wanda ya na daya daga cikin ayarin Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa rikicin ya faro ne a lokacin da wasu bata-gari da ba a san ko su wanene ba dauke da makamai su ka yi kokarin tare tawagar Sarkin , da zummar Wai sarkinba ba zai wuce ta Kofar-Kudu ba.
“Bayan wancan yunkuri, hakan tasa yan tawagar Sarkin su ka tarwatsa su, sannan Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya zo ya wuce salun alun, Amma ba tun an Kai musu hari haka kawai ba Gaskiya be su ne suka tsikane mu”. Inji Mukhtar Dahiru.
Ya jaddada cewa rikicin ne ya sa ‘yan sanda suka shiga tsakani, inda suka tarwatsa ’yan batagarin da barkonon tsohuwar wato Tea rGas.
Kokarin samun karin bayani daga ‘yan sanda game da lamarin ya ci tura.