Ganduje da Ma’aikatar Muhalli sun Mika sakon ta’aziyyar Sarkin Tsaftar Kano

Date:

Daga Sani Magaji Garko

Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya Mika sakon taaziyyar sa ga al’ummar jihar Kano da kuma Yan uwa da iyalai bisa rasuwar Sarkin tsaftar Kano Alhaji Jafaru Ahmad Gwarzo.

Cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Abba Anwar ya fitar ta ambato Ganduje Yana Mika taaziyyar sa ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero bisa rasuwar wacce ya bayyana ta a Matsayin babban rashi ga al’ummar jihar Kano.

Sanarwar ta ambato Ganduje na cewa marigayin yayi fice wajen yaki da cutar shan-inna (Polio) da yaki da matsalolin Muhalli da ma yaki da yaduwar cututtuka a tsakanin al’umma.

A lokacin Yana sarki tsafta yayi yawo a guri-guri cikin loko da sakon Kano da nufin tabbatar da tsaftar Muhalli da ta jiki da gudanar da gangamin wayar da kan al’umma muhimmancin kula da lafiya da kuma kayayyakin da mutane ke ci”.

Rasuwar sa ta bar wani katon gibi Mai wahalar cikewa a Kano, saboda mutum be jajircewa, haziki Mai tausayawa na kasa da kuma tabbatar da doka”.

A wani labarin Kuma, Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya Mika sakon taaziyar sa ga Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero bisa rasuwar Sarkin tsaftar Kano Alhaji Jafaru Ahmad Gwarzo Kuma Mai bawa gwamna shawara a kan harkokin tsaftar Muhalli.

Marigayi Sarkin tsaftar ya rasu ne a kasar Saudiya inda ya tafi neman magani.

Cikin wata sanarwa Mai dauke da sa hanin jami’in hulda da jamaa na maaikatar Muhallin Sanusi Abdullahi Kofar Na’isa ya fitar ta ambato kwamishinan na bayyana Sarkin tsafta a Matsayin jajirtacce Kuma Dan kishin kasa da cigaban al’umma Wanda ya bar wani gibi Mai wahalar cikewa.

Dakta Kabiru Getso ya kuma Mika sakon taaziyar sa ga iyalai da Yan uwan marigayin inda yayi fatan Aljanna ta kasance makomar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...