Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi kuma shugaban Kwamitin kasafin Kudi na majalisar  Hon. Abubakar Kabir Bichi, ya raba sabbin motocin bas masu daukar mutane 16 ga jami’o’i da kwalejojin ilimi a Kano da taraktoci guda  11 don inganta noma da Ilimi a Kano .

Kadaura24 ta rawaito wakilai daga jami’o’i da manyan Makarantu daban-daban na jihar Kano sun halarci taron rabon kayayyakin, wanda aka gudanar a ranar Litinin a garin Bichi.

InShot 20250309 102512486
Talla

Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi ya samu wakilcin shugaban kwamitin ilimi Dakta Habibu Usman Abdu da manyan  hadimansa na majalisa Sabo Ilyasu Saye da Zahraddeen Kabir da sauransu .

Manyan makarantun da suka ci gajiyar shirin sun hada da Jami’ar Bayero (BUK), wacce ta samu motocin bas 2, jami’ar Northwest ta Kano motocin bas guda biyu, Jami’ar Aliko Dangote dake Wudil motocin bas guda biyu, FCE  Bichi bas guda biyu, Jami’ar Tarayya ta Yusuf Maitama Sule take Kano bas daya, Ibrahim Ayagi College of Health Science Dawakin Tofa, Aminu Kano College of Islamic Legal bas daya, Aminu Kano College of Islamic and Legal studies bas, Sa’adatu Rimi college of Education bas daya.

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

An kuma raba taraktoci goma sha daya da injinan gurbi na zamani guda 4 ga mazabun goma sha daya dake fadin karamar hukumar Bichi.

Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi ya ce ya bayar da motocin ne ga manyan makarantu da nufin saukaka kalubalen sufuri a makarantun .

Ya kara da cewa taraktoci goma sha daya da injinan girbin da aka raba ya bayar da su ne don inganta harkokin noma a mazabu goma sha daya da ke karamar hukumar Bichi.

Yayin taron an zayyano wasu daga cikin aiyuka da Hon. Abubakar Kabir Bichi ya yi na tallafawa fannin ilimi .

Irin wadannan ayyukan tallafi da Hon. Abba Bichi ya ke yi a fannin ilimi da dai sauran su ne suka sa Jami’ar Tarayya, Kashere dake Jihar Gombe da Jami’ar Tarayya ta Dutsin-ma dake jihar Katsina suka baiwa Abubakar Kabir Bichi digirin girmamawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...