Daga jafar adam
Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam ya bukaci al’ummar jihar Kano da su dage da yin addu’o’i na musamman ga Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir don cigaba da samun Nasarar kawowa jihar cigaba .
” Yadda Allah ya taimake mu ya ba mu gwamna Mai kishinmu kuma mai kaunar ganin jihar Kano ta cigaba, don haka ha abun da ya kamace mu face mu dage da taya shi da Addu’o’in Allah ya cigaba da yin riko da hannayensa don ya cigaba da kawowa jihar Kano cigaban da zamu cigaba da alfahari da ita”.

Sharu Namalam ya bayyana hakan ne yayin katamar karatun Alqur’ani mai girma da addu’o’i na musamman da yan kasuwarsu suka shiryawa gwamnan saboda cikarsa Shekaru biyu akan karagar mulkin Kano .
Ya ce gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta shekara biyu tana aiyukan alkhairi a lungu da sako na jihar Kano, “don haka muka ga decewar mu shirya Wannan addu’a don yiwa Allah godiya da ya tabbatar da gwamnatinsu kuma ya kara baiwa gwamnan Hikima da basirar kawo cigaba jihar Kano .
Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC
” An Karanta Alqur’ani a wurare daban-daban shi ne kuma muka hadu a Wannan wajen don yin karama, kuma Muna godiya ga Allah ya nuna mana Wannan waje sannan muna addu’ar Allah ya karawa Mai girma gwamna Shekaru masu albarka ya kuma kara masa lafiya da mu baki daya”. Inji Sharu Namalam
Sharu Abdullahi Namalam ya kuma yi fatan al’ummar jihar Kano za su cigaba da baiwa gwamna Abba Kabir Yusuf hadin kai da goyon bayan kuma ci rika yi masa addu’a don ya cigaba da yi musu aiyukan alkhairi a birni da karkara.