Nasarar Abba Gida-gida ta wucin gadi ce – Ganduje

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce zasu ƙalubalanci sakamakon zaben gwamnan Kano a kotun sauraren kararrakin zabe.

 

Kadaura24 ta rawaito gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai akan shawarwarin da zaɓaɓɓen gwamnan kano ya baiwa masu gine-gine a filayen gwamnati da kuma bankuna da masu bada bashi.

Ba zan biya duk wani bashi da Ganduje ya ciyo bayan zabe ba – Shawarar Abba Gida-gida ga bankuna

 

Ganduje yace sun shirya tsaf don tafiya kotu don haka ya ce koda sabon zaɓaɓɓen gwamnan na kano ya fara tafiyar da gwamnatin Kano zata kasance ta wucin gadin ne domin suna da kwarin gwiwar samun nasara a kotu.

Hadimin Ganduje Aminu Dahiru ya baiwa wasu matasa tallafin karatu a Kano

 

” Yana maganganu kamar shi ne gwamnan kano yanzu, ina so ya Sani cewa Shawarwarin da yake baiwa mutane basu da tushe ballantana makama”. Inji Ganduje

 

Ko da aka tambaye shi game da shirin mika mulki, gwamna Ganduje yace zasu gudanar da taron majalisar zartarwar Kuma daga nan ne zasu tattauna akan batun tare da fitar da sunayen wadanda zasu yi aikin don ganin an mika mulkin ba tare da wata matsala ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugaban K/H Garun Mallam zai Raba Audugar Mata 500 ga Makarantun Sakandiren Matan yankin

Daga Safiyanu Dantala Jobawa Shugaban karamar hukumar garun mallam Aminu...

Inganta Noma: Sanata Barau zai tallafawa Matasa 558 daga Arewa maso yammacin Nigeria

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Kwamitin Majalisar Wakilai ya gabatar da shawarar kara Jihohi 31 a Nigeria

Daga Maryam Muhammad Ibrahim Kwamitin majalisar wakilan Nigeria mai kula...

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...