Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 11 da ke Bompai ta yanke wa Umar Auwal da Yakubu Dayyabu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin kashe wata mata, Fatima Abubakar, da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Ciranci da ke Kano.
Mai Shari’a Nasiru Saminu ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2026, bayan nazarin shaidu da hujjojin da aka gabatar a gaban kotun.
Read also: Da dumi-dumi: Kotun daukaka kara ta yi watsai da bukatar Abba Kabir Yusuf

Kotun ta samu Umar Auwal, wanda aka fi sani da Breaker, da Yakubu Dayyabu, wanda ake kira Wawo, da laifin kashe Fatima da ’ya’yanta shida a ranar 17 ga Janairu, 2026.
A sakamakon haka, kotun ta yanke wa kowannensu hukuncin kisa ta hanyar rataya sau bakwai, bisa la’akari da kisan mutanen bakwai.
Read also: Har yanzu babu wani mutum da ya kamu da cutar Anthrax a Najeriya – NCDC
Haka kuma, kotun ta yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai bisa laifukan haɗa baki da fashi da makami.
Sai dai kotun ta wanke Isiyaku Yakubu tare da sallamarsa daga zargin haɗa baki wajen kisan mutanen bakwai.

Read also: Da dumi-dumi: Kotun zaɓen shugaban ƙasa ta kori ƙarar Peter Obi
Tawagar masu gabatar da ƙara ta ƙunshi Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabir Maude, tare da Barrister Salisu Muhammad Tahir.
Yayin da Barrister J. I. Musa da Barrister A. I. Baba suka wakilci waɗanda ake ƙara.