Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sauya wa wasu kwamishinoni ma’aikatun da suke jagoranta, tare da bayyana sabbin mukaman kwamishinonin da aka nada.
A cikin sabon tsarin rabon ma’aikatun, an mayar da Hon. Ibrahim Abdullahi Waiya zuwa Ma’aikatar Matasa, yayin da Hon. Safyanu Kachako aka mayar da shi Ma’aikatar Muhalli.
Read also: 2023: Ni Ba na Neman Kujerar Gwamnan jihar Kano – Ali Haruna Makoda

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin taron rantsar da sabbin kwamishinonin da majalisar dokokin jihar Kano ta amince gwamnan.
Sauran kwamishinonin da aka ware wa ma’aikatu sun hada da:
1. Hon. Yushau Soja – Ma’aikatar Tsaro.
2. Hon. Idris Garba Mustapha – Ma’aikatar Ayyuka na Musamman.
3. Hon. Muntari Ishaq Yakasai – Ma’aikatar Jinƙai.
4. Hon. Ibrahim Namadi Dala – Ma’aikatar Kasuwanci.
5. Hon. Ibrahim Tsanyawa – Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha.
6. Hon. Safyanu Kachako – Ma’aikatar Muhalli.
7. Hon. Ibrahim Abdullahi Waiya – Ma’aikatar Matasa.
Read also: Hasashen yanayin da zai kasance yau talata a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
8. Farfesa Sani Lawan Malumfashi – Ma’aikatar Ilimi mai zurfi