Dan takarar kujerar Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Wudil da Garko a karkashin jam’iyyar ADC Hon. Barrister Ahmad Sani Bawa, ya kaddamar da Kwamitin Dattawa, Kwamitin Shugabanci da kuma Kwamitocin Yakin Neman Zabensa.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a garin Wudil, inda jiga-jigan jam’iyyar ADC daga matakin jiha da na kananan hukumomi suka halarta.

Da yake jawabi a wajen taron, Barr. Ahmad Sani Bawa ya ce kafa kwamitocin ya zama wajibi domin tabbatar da tsari da hadin kai a cikin tafiyar, tare da tabbatar da nasarar jam’iyyar ADC a zabe mai zuwa na 2027.
A cewarsa, kwamitin dattawan zai kasance uba ga tafiyar, yayin da kwamitin shugabanci zai tafiyar da harkokin yau da kullum, sai kwamitocin yakin neman zabe da za su yi aiki a matakin mazabu da kauyuka.
Mun kaddamar da wadannan kwamitoci ne don mu tabbatar da cewa kowa yana cikin tafiyar. Manufarmu ita ce kawo sauyi na gaskiya ga al’ummar Wudil da Garko. ADC ita ce jam’iyya mai fata, kuma tare da goyon bayan dattawanmu da matasanmu za mu kai ga nasara,” in ji Barr. Bawa.
Ya yi kira ga mambobin kwamitocin da su yi aiki da gaskiya da rikon amana, tare da bude kofa ga kowa da kowa.
Shugaban jam’iyyar ADC na Jihar Kano da ya halarci taron ya bayyana Barr. Bawa a matsayin dan takara nagari da jam’iyyar ke alfahari da shi, yana mai cewa jam’iyyar na da kwarin gwiwar lashe kujerar Wudil/Garko.
Hajiya Aisha Captain Walfare Ta Yabawa Dan Takarar ADC Jiga-jigar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Kano, Hajiya Aisha Captain Walfare, ta yabawa dan takarar kujerar Majalisar Tarayya na Wudil da Garko, Hon. Barrister Ahmad Sani Bawa, bisa namijin kokari da tsari da ya nuna wajen kaddamar da kwamitocinsa na yakin neman zabe.
Hajiya Aisha Captain Walfare ta bayyana hakan ne a lokacin da take jawabi a wajen bikin kaddamar da Kwamitin Dattawa, Shugabanci da Kwamitocin Yakin Neman Zaben dan takarar da aka gudanar a Wudil.
A cewarta, Barr. Ahmad Sani Bawa ya nuna cewa shi matashi ne mai hangen nesa da kishin al’umma, wanda ya cancanci wakilcin al’ummar Wudil da Garko a Majalisar Tarayya.
Na zo nan na ga tsari na kwarai. Dan takarar namu ya nuna girma ga dattawa ta hanyar kafa kwamitin dattawa, ya nuna shugabanci na gari, kuma ya shirya dabarun yakin neman zabe. Wannan shi ne abin da muke kira siyasa mai inganci. Muna alfahari da shi a jam’iyyar ADC ta Kano,” in ji ta.
Ta kara da cewa jam’iyyar ADC a Kano na samun karbuwa ne saboda irin mutane masu gaskiya da aiki tukuru da ke shigowa cikinta kamar Barr. Bawa.
Read also: Cin Hanci: Yan Sanda Sun Gurfanar da Jarumar Kannywood, Amal, a Gaban Kotu
Read also: Sanata Barau Da Hadin Kan APC a Kano – Abba Anwar
Read also: NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Hajiya Aisha ta yi kira ga mata da matasa na Wudil da Garko da su fito kwansu da kwarkwata su marawa jam’iyyar ADC baya, domin ita ce kadai jam’iyyar da za ta kawo sauyi na gaskiya.
Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyyar ADC na jiha da kananan hukumomi, da magoya baya daga Wudil da Garko.