2023: Ni Ba na Neman Kujerar Gwamnan jihar Kano – Ali Haruna Makoda

Date:

Daga Zara Jamil Isa

 

Shugaban Ma’aikatan fadar Gwamnatin Jihar Kano Dr Ali Haruna Makoda ya bayyawa duniya cewa shi har Yanzu bashi da burin tsayawa takarar Kujerar Gwamnan Kano ko ma Wata Kujerar mulki.

KADAURA24 ta rawaito Dr. Ali Haruna Makoda ya bayyana hakan ne yayin da ya yake gabatar da Jawabi a wajen taron Kungiyar tsofaffin Daliban Makaranatar Sakandire ta kafin Hausa yan aji na Shekara ta 1988.

Ali baya neman wata Kujerar mulki a Shekarar ta 2023 sai Kujerar da Allah ya zaba Masa wadda zata Zama alkhairi a gare ni da ku da duk al’ummar Jihar Kano baki daya,tun da zabin Allah shi ne dai-dai”. Dr Ali Makoda

Dr. Makoda ya roki ‘ya’yan Kungiyar da su taya su da yin addu’o’in kammala aikin da aka dora musu lami Lafiya Kamar yadda Suka Fara Lafiya.

An dade dai ana kiraye-kirayen Shugaban Ma’aikatan ya fito neman kurejar Gwamnan jihar Kano Saboda irin Gudunmawar da ake ganin zai iya bayar wajen cigaban Jihar nan idan ya Sami dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...