Ba Sai Da Muƙami Ake Taimakon Al’umma Ba — MD Hassan Ya Yabi Matawallen Gwagwarwa Kan Tallafawa Mutane 327

Date:

‎Ƙungiyar Abba Gida-Gida Machineries ta Jihar Kano ta bai wa mutum 327 tallafin jari domin ƙarfafa musu guiwa wajen dogaro da kansu da kuma bunƙasa ƙananan sana’o’i.
‎
‎Jagoran ƙungiyar a jihar Kano, Barr. Ibrahim Isa Matawallen Gwagwarwa, ne ya jagoranci rabon tallafin a wani babban taro da aka gudanar a Kano ranar Lahadi.
‎
‎Da yake jawabi a wajen taron, Matawallen Gwagwarwa ya bayyana cewa tallafin na daga cikin ƙoƙarin ƙungiyar na tallafa wa manufofin gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, musamman ta fuskar yaƙi da talauci, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’umma.

IMG 20260704 WA0007
Talla

‎
‎Ya ce waɗanda suka amfana da tallafin sun haɗa da mata, matasa da masu ƙananan sana’o’i, waɗanda aka ba kuɗaɗen domin bunƙasa sana’o’insu ko kuma fara sababbi.
‎
‎A cewarsa, ƙungiyar ta ɗauki wannan mataki ne domin taimaka wa al’umma su samu hanyoyin dogaro da kansu, tare da bayar da gudunmawa wajen cimma manufofin gwamnatin jihar.
‎
‎> “Mun yanke shawarar bayar da wannan tallafi ne saboda muna son al’umma su dogara da kansu. Gwamnatin Abba Gida-Gida tana ƙoƙari wajen raya ƙasa, mu kuma a matsayinmu na ƙungiyar da ke fafutukar ganin ta samu nasara, za mu ci gaba da bayar da namu gudunmawar,” in ji shi.
‎
‎
‎
‎Matawallen Gwagwarwa ya ƙara da cewa ƙungiyar Abba Machineries za ta ci gaba da gudanar da shirye-shirye irin wannan a faɗin jihar Kano domin tallafa wa al’umma da kuma isar da manufofin gwamnati zuwa matakin ƙasa.
‎
‎Ya jaddada cewa tallafawa mata da matasa wajen samun abin dogaro da kai na daga cikin muhimman hanyoyin rage talauci da bunƙasa tattalin arzikin al’umma.
‎
‎MD HANSAN YA YABA DA ƘOƘARIN MATAWALLEN GWAGWARWA
‎
‎A nasa jawabin, ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon. MD Hansan, ya yaba wa Barr. Ibrahim Isa Matawallen Gwagwarwa bisa ƙoƙarinsa na tallafa wa al’ummar mazabar Gwagwarwa da sauran masu buƙatar taimako.
‎
‎MD Hansan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen rabon tallafin jarin ga mutum 327 da ƙungiyar ta gudanar a Kano ranar Lahadi.
‎
‎Ya ce abin da Matawallen Gwagwarwa ya yi abin a yaba ne, domin ya nuna kishin al’umma da jajircewa wajen ganin mata da matasa sun samu abin dogaro da kai, duk da cewa ba shi da wani muƙamin gwamnati a halin yanzu.
‎
‎A cewarsa, wannan mataki ya nuna cewa taimaka wa al’umma ba sai mutum ya riƙe muƙamin gwamnati ba, domin kowa na iya bayar da gudunmawa gwargwadon ƙarfinsa.
‎
‎> “Wannan abin koyi ne. Barrister ya nuna mana cewa ba sai kana da muƙamin gwamnati ba kafin ka taimaki al’umma. Abin da ya yi wa ‘yan’uwanmu na mazabar Gwagwarwa ya cancanci yabo. Muna tare da shi dari bisa ɗari wajen ganin an ciyar da jihar Kano gaba,” in ji MD Hansan.
‎
‎
‎
‎Ya ƙara da cewa irin wannan shiri na taimakawa wajen rage zaman kashe wando, ƙarfafa gwiwar matasa da kuma bunƙasa tattalin arzikinsu ta hanyar samar musu da jari da za su iya amfani da shi wajen gudanar da sana’o’i.
‎
‎Saboda haka, ya yi kira ga sauran masu hannu da shuni da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su yi koyi da wannan mataki, ta hanyar tallafa wa marasa ƙarfi da samar da hanyoyin dogaro da kai.
‎
‎Haka kuma, MD Hansan ya sake jaddada goyon bayansa ga manufofin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana mai cewa zai ci gaba da mara wa duk wani shiri da ke da manufar inganta rayuwar al’umma baya.
‎
‎FB IMG
‎
‎Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikinsu, inda suka gode wa jagoran ƙungiyar bisa wannan tallafi da suka ce zai taimaka musu wajen bunƙasa sana’o’insu da inganta rayuwarsu.
‎
‎Sun kuma yi alƙawarin yin amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata domin cimma manufar da aka bayar da su.
‎
‎Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, shugabannin ƙungiyoyi da kuma magoya bayan gwamnatin jihar Kano.
‎

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubawan da aka cimma tsakanin Gwamnatin tarayya da Kungiyar Kwadago

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta amince da biyan tallafin sufuri...

Sardaunan Gombe: Hasken Rana Leka Gidan Kowa: Jamil Gwamna, Jagoran Da Yake Da Burin Cigaba Da Gina Jihar Gombe – Shawai

Daga Ibrahim Sani ShawaiDaga cincirindon jama’a na grassroots, zuwa...

Majalisar dokokin Kano ta amince da naɗin sabbin kwamishinoni shida da gwamna Abba ya tura mata

Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da naɗin sabbin...