Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, da ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Abdulsalam Gwarzo, domin shiga zaɓen 2027 kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Sai dai hukumar ta ce amincewar tasu tana ƙarƙashin hukuncin ƙarshe da kotu za ta yanke kan shari’o’in da suka shafe su.
Read also: Da dumi-dumi: Kotun Ɗaukaka Kara ta Yanke Hukuncin Zaɓen Gwamnan Bauchi

Wata majiya a INEC ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa hukumar ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 69 daga jam’iyyun siyasa kan cire sunayen wasu ’yan takara daga jerin sunayen waɗanda za su fafata a zaɓen gwamna da na ’yan majalisun jihohi.
Read also: Yan Sanda sun ceto mutumin da aka kulle a daki tsawon shekaru 20
Ta ce an amince da ƙorafe-ƙorafe 36, yayin da aka yi watsi da sauran.
Majiyar ta tabbatar da cewa Pantami ya samu nasara, yayin da ta ce amincewa da Gwarzo za ta dogara da hukuncin kotu.
Haka kuma, hukumar ta yi watsi da ƙorafin ɗan takarar gwamnan Ogun na PDP, Ladi Adebutu, wanda ya nemi a sake duba cire sunansa daga jerin ’yan takara.
Read also: Za mu samar da sabbin wuraren kasuwanci a Kano don rage cunkoso a birnin jihar – Abba Gida-gida
INEC ta bayyana cewa cire sunayen ’yan takarar ya samo asali ne daga rashin cika wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026, musamman batun miƙa rajistar mambobin jam’iyyu ga hukumar.

Ana sa ran INEC za ta fitar da sanarwar hukuma kan sakamakon nazarin ƙorafe-ƙorafen.