Daga Aliyu Abdullahi Danbala
Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta nada Kwamared Abbas Ibrahim a matsayin dan kwamintin amintattu na kungiyar .
Shugaban kungiyar na Kasa Kwamared Alhassan Yahaya ya bayyana nadin yayin bikin cikar kungiyar Shekaru 70 da kasuwa, wanda aka gudanar a Abuja .

Alhassan Yahaya ya ce sun baiwa Abbas Ibrahim mukamin ne saboda chanchantarsa da kuma gudunmawar da ya baiwa kungiyar don cigabanta.
Abbas Ibrahim tsoho shugaban kungiyar yan Jarida ta kasa reshen jihar Kano, ƙwararren Dan Jarida ne da yake aiki a gidan Radio Jihar Kano .