Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, a gidansa da ke garin Dutsin-Ma, Jihar Katsina.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare, a ƙofar gidan malamin, inda maharan suka buɗe masa wuta tare da wani amininsa.
Read also: Ana zargin Hisbah da daurawa wata yarinya aure da Dan China bayan ya yi mata ciki

Bayan harin, an garzaya da su zuwa Asibitin Dutsin-Ma domin ba su agajin gaggawa, sai dai daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu.
Read also: NNPC ya fara jigilar Iskar Gas zuwa ƙasar China da Japan
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a san dalilin da ya sa aka kashe malamin ba, yayin da har yanzu ba a samu cikakken bayani kan yadda harin ya faru ba.
Kisan ya jefa al’ummar garin Dutsin-Ma cikin alhini, musamman mabiyan Sheikh Yahaya Masussuka da sauran mutanen da suka san shi.
Read also: CBN ya bayyana matakan da yake bi har Dala take karyewa a Nigeria
Rundunar ’yansanda ta tabbatar wa da DW Hausa mutuwar malamin, duk da cewa ba a fitar da cikakken bayani kan lamarin ba.

Kadaura24 ta rawaito tuni dai gwamnan jihar Katsina Umar Dikko Radda ya yi Allah-wadai da kisan malamin kuma ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano Wadanda suka aikata laifin.