‎INEC ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar gwamna a jihohin Najeriya, Amma ba a ga sunan Gwarzo da Pantami ba

Date:

‎
‎
‎Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta fitar da jerin sunayen mutanen da zasu yiwa jam’iyyu takarar gwamna a jihohi 28 na ƙasar da zasu shiga babban zaɓe na shekarar 2027.
‎
‎Sai dai rashin ganin sunayen wasu daga cikin jiga-jigan ƴan siyasa a wasu jihohi ta haifar da muhawara, inda wasu ke alaƙanta hakan da kuskure daga INEC, yayin da wasu ke cewa hukuncin da kotu ta yi na baya-bayan nan ne ya shafi wasu.

IMG 20260704 WA0007
Talla

‎
‎A jihar Kano dai, ba a ga sunan Kwamred Aminu Abdulsalam Gwarzo ba, wanda shi ne mai yiwa jam’iyyar adawa ta NDC takarar gwamna, yayin da acan Gombe aka nemi sunan tsohon ministan sadarwar ƙasar Malam Isa Pantami na PDP aka rasa cikin jerin ƴan takarar gwamna a jihar.
‎
‎Kodayake tuni wasu jam’iyyu suka fara fitar wa sanarwar kwantarwa da magoya bayansu hankali, inda suka ce zasu bibiyi lamarin don gano musabbabin rashin ganin sunayensu.
‎
‎Ko a jihar Kano ma , shugaban NDC na jihar Hussaini Isa Mai Riga ya ce tuni wakilan jam’iyyar NDC suka ofishin hukumar zabe ta Kasa dake Abuja domin tabbatar da sun gyara kuskuren da suka yi.
‎
‎”Mu a saninmu Com. Aminu Abdussalam Gwarzo da Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso mu ka sani a matsayin yan takararmu, Kuma jam’iyyar NDC na iya kin kokarinta don ganin an dawo da sunan yan takarar”. a cewar mairiga
‎
‎Ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar NDC na jihar Kano da su kwantar da hankulansu domin komai zai daidaita nan ba da jimawa ba.

FB IMG
‎
‎A ƴan kwanakin da suka gabata ne, kotun ƙoli a Najeriya ta yanke wani hukunci game da lokacin da ya kamata jam’iyyu su miƙa wa INEC sunayen ƴan takarar su, wanda ake ganin zai shafi wasu masu takara musamman waɗanda suka sauya sheƙa zuwa wata jam’iyyar bayan rashin nasarar a zaɓen cikin gida na jam’iyyun da suke tun farko.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Yan sanda sun hana taron Tinubu Must Go a Kano

‎ ‎ ‎Rundunar ’yansandan jihar Kano ta tarwatsa masu shirin gudanar...

Jami’ar Baze ta jaddada muhimmancin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa

Jami’ar Baze da ke Abuja ta kammala bikin makon...

‎Kano da Amurka Sun Ƙulla Sabuwar Alakar Haɗin Gwiwa kan Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

‎ ‎Rundunar haɗin gwiwa dake yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya sulhunta Sanata Barau da Abba Bichi

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sasanta mataimakin...