Rundunar ’yansandan jihar Kano ta tarwatsa masu shirin gudanar da gangamin ‘Tinubu Must Go.
Abba Hikima Fagge, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga magoya bayan gangamin.

Abba Hikima ya zargi Kwamishinan ’Yan Sandan Kano da tura jami’an tsaro domin rufe wurin da suka tanada don gudanar da taron.
Hikima ya bayyana matakin a matsayin rashin adalci da kuma keta dokokin ƙasa, tare da zargin nuna son kai wajen gudanar da ayyukan tsaro.
”Tsoro suke ji kada muyi taro mu basu kunya, tun karfe 9 na safe suka tare hanyoyi, suka garkame wajen taron, uma wai a mulkin dimukuradiyya”. inji Abba Hikima
Read also: Gina Jami’oi masu Zaman kansu zaisa dalibai samun guraben Karatu – Sarkin Kano Bayero
Read also: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kammala sauraron shari’ar zaɓen gwamnan jihar Nasarawa
Read also: 2023: Duk ƙuri’un da Buhari ke samu a Arewa sun zama na Kwankwaso, in ji Kofa

Ya kuma yi kira ga rundunar ’yan sandan da ta guji abin da ya bayyana a matsayin kare muradun jam’iyyar APC, yana mai cewa ya kamata jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu ba tare da nuna bambancin siyasa ba.